Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: Majalisar dokokin Najeriya ta tafi hutu ta bar baya da ƙura kan ƙudurori
Bisa dukkan alamu matakin amincewa da wasu muhimman ƙudurorin dokoki da ƴan majalisun dokokin Najeriya suka yi ya bar baya da ƙura, kasancewar babbar jam'iyyar hamayyar kasar, wato PDP ta ce za ta ƙalubalanci wasu kudurori biyu.
Kudurorin na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziki da kuma dimokuraɗiyyar kasar.
Wannan na faruwa ne yayin da ƴan majalisar suka fara hutunsu na shekara-shekara.
A makon jiya ne ƴan majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da ƙudurin gyara ga dokar zaɓe a wani yanayi mai taƙaddama, saboda ƴan PDP sun ce sai an sanya batun amfani da laturoni wajen kaɗa ƙuri'a da kuma sanar da sakamakon zaɓe.
Kudurin da bangarori biyu da majalisar suka amince da shi bai tanadi cewa dole a yi amfani da na'urar kwamfuta wajen kaɗa ƙuri'a da kuma aikewa da sakamakon zaɓe zuwa cibiyar tattara sakamako ba.
Haka nan majalisun sun amince da ƙudurin yin garambawul ga harkar man fetur wanda shi ma wasu ƴan PDP ke nuna tirjiya a kai.
Suna neman a ƙara kudaden da kamfanoni za su dinga keɓe wa al'umomin da ake haƙar mai a yankunansu zuwa kashi bakwai cikin dari na jarin kamfanonin, amma majalisun suka yi watsi da wannan bukatar.
Majalisun dai sun amince da a riƙa kebe kashi uku cikin dari ne ga al'umomin a sabuwar dokar, wanda ke nufin an yi wa al'umomin karin rabin kashi daya a kan adadin da aka saba ware masu.
Wasu labaran masu alaƙa
'PDP Za ta kai kara kotu'
To sai dai duk da cewa Majalisar Dokokin ta kasa ta amincewa da ƙududorin biyu ta hanyar kaɗa ƙuri'a tsakanin 'yan majalisar, bisa dukkan alamu jam'iyyar PDP mai hamayya ba ta gamsu da matakin bangarori biyu na majalisar ba.
Sakamakon rashin gamsuwar, jam'iyyar PDP ta ce za ta ƙalubalanci matakin a kotu.
Jam'iyyar APC mai mulki ce ke da rinjayen wakilai a cikin ɓangarorin biyu na majalisa - wato Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma Majalisar Dattawa.
An ambato shugaban PDP na kasa, Mr Uche Secondus na cewa ƙin amincewar majalisun dokokin a sanya shaɗarar doka da za ta wajabta aikewa da sakamakon zabe zuwa cibiyar tattara sakamako ta hanyar amfani da laturoni, alama ce ta yadda APC "ba ta da niyyar ƙarfafa dimokuradiyyar Najeriya."
PDP ta ce tabbatar da zaɓe nagari, cikin ƴanci da kamanta adalci, shi ne gimshikin dimokuradiyya.
Mista Secondus ya bayyyana cewa "PDP za ta dauki dukkan matakan shari'a da suka wajaba" don ganin matakin ƴan jam'iyyar APC a majalisar bai tabbata ba.
Tun farko dai PDP ta ce ba ta goyon bayan wasu sassa na shi ma ƙudurin dokar yi wa harkar man fetur a Najeriya garambawul.
Musamman yadda majalisar dokokin ta kasa ta amince da 3% a matsayin kason da za a riƙa keɓe wa al'umomin da ake haƙo man fetur a yankunansu.
PDP da kuma wasu gwamnonin kudancin Najeriya na ganin kamata ya yi adadin kason ya ruɓanya hakan.
'Yan Jam'iyyar APC sun yi wa PDP raddi
Kawo yanzu dai babu tabbas kan lokacin da jam'iyyar ta PDP za ta shigar da kara, da kuma irin hujjoji da zata gabatar a gaban kotu. To amma bisa dukkan alamu lamarin na tayar da kura.
Sai dai ƴan APC na cewa PDP na neman nade tabarmar kunya ne kawai domin kuwa tun da har majalisa ta riga ta amince da ƙudurorin, to batun zuwa kotu ba zai yi tasiri ba.
Sanata Abdullahi Adamu, dan majalisar dattawa daga jam'iyyar APC mai mulki ya ce ''sambatu'' kawai shuwagabanni na jam'iyyar PDP ke yi, da nufin nuna wa talakawa masu goyon bayansu cewa wakilansu a majalisa ba su bayar da kai ba.
Sanata Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ba sa tsoron zuwa kotu domin ''kotu ta kowa ce'' kuma duk wanda ya ji an yi masa ba daidai ba yana da 'yancin zuwa kotu.
To amma ya ce a ganinsa lamarin ƙudurorin bai bar baya da ƙura ba.
Sanata Abdullahi ya ce kamata ya yi 'yan PDP su haƙura, su haɗa kai da sauran ƴan majalisa domin ciyar da kasa gaba - domin kuwa dama lamarin majalisa, batu ne na masu rinjaye ake amfani da ra'ayinsu.
Ya musanta zargin ƙumbiya-ƙumbiya da rashin nuna gaskiya wajen amincewa da ƙudurorin a majalisa, yana mai cewa an bi ƙa'ida.
Kawo yanzu dai abin da ya rage don ƙudurorin sun zamo cikakkun dokoki shi ne a miƙa wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kansu.
A cewar Abdullahi Adamu, abin da aka amince da shi a majalisa ya zauna kuma ''mai kwance wannan abu kawai sai Allah da ya yi mu.''
Kudurorin na da matuƙar muhimmanci ga makomar Najeriya
Wannan dambarwa tsakanin manyan jam'iyyun siyasar Najeriya dai ta bayyana ƙarara tun lokacin da ake tafka muhawara a cikin majalisa.
A wasu lokutan sai da aka bai wa hamata iska tsakanin 'yan majalisa sakamakon saɓanin ra'ayi kan ƙudurorin.
Kudurorin dokokin guda biyu na daga cikin mafiya muhimmanci da majalisar dokokin ta kasa ta tafka muhawwara a kansu ta kuma amince da su cikin aikinta na tsawon shekaru.
Misali, shirin dokar yin garambawul ga harkar man fetur a Najeriya ya shafe fiye da shekaru goma a gaban majalisar, inda duk yunkurin da aka yi a baya na amince da shi ya faskara.
Tattalin arzikin Najeriya dai ya dogara ne kusan kacokam kan albarkatun man fetur.
Wannan ya sanya duk abin da ya shafi bangaren man fetur kan shafi kasar, da kuma janyo muhawara tsakanin shugabanni da kuma talakawa.
Shi ma ƙudurin yi wa dokokin zabe gyaran fuska na da muhimmanci ga makomar Najeriya ganin kasar na tunkarar muhimman manyan zabuka a 2023 - wato nan da kasa da shekaru biyu masu zuwa.
Abin da wannan kuma ke nufi shi ne dokar za ta yi tasiri kan tafiyar dimokuradiyyar kasar.
A cikin watan Satumba ne dai ake sa ran ƴan majalisar za nsu kammala hutunsu kana su koma bakin aiki na zaman majalisa.
Babu tabbas kan abin da zai kasance yayin da 'yan majalisar wakilan da 'yan majalisar dattawa suka dawo daga hutun.