Rikicin Tigray na iya daidaita mutum miliyan tara - MDD

A still image taken from a video shows Ethiopian Prime Minister Abiy Ahmed addressing the nation in Addis Ababa, Ethiopia November 4, 2020. Ethiopia Broadcasting Coporation

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Abiy Ahmed ya yi wa kasar Habasha jawabi gabanin tura sojoji yankin Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya kori manyan jami'an gwamnatinsa yayin da rikici ke kara kamari a yankin Tigray na arewacin kasar.

Cikin jami'an da ya kora akwai babban hafsan hafsoshin sojin kasar, da shugaban ma'aikatar leken asiri da ministan harkokin waje, wadanda bai yi wata-wata ba ya maye gurbinsu da wasu jami'an.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaki ya barke tsakanin sojojin gwamnatin tarayyar kasar da na yankin na Tigray a wurare takwas.

Gwamnatin Habasha ba ta sanar da dalilanta na korar manyan jami'an gwamnatin ba, wadanda aka kora a rana ta biyar ta yakin da gwamnatin ta kaddamar kan yankin na Tigray.

Bayanan bidiyo, Bidiyon abu huɗu da kuke buƙatar sani kan rikicin ƙasar Habasha
Tigray special forces in federal military uniforms
Bayanan hoto, Wadannan dakarun yankin Tigray sun kwace wani sansanin sojojin kasar a farkon makon nan

Rahotanni na cewa gomman mayakan Tigran sun rasa rayukansu, kuma wasunsu sun jikkata, har an kai wasunsu zuwa asibitoci a yankin Amhara mai makwabtaka da yankin na Tigray.

MDD ta ce wannan yakin na iya tilastawa mutum miliyan tara barin muhallansu da garuruwansu -- kuma akwai kayayyakin jin kai da ba za su kai ga al'umomin da ke bukatarsu ba.

Ethiopia Gen Adem Mohammed pictured in February 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gen Adem Mohammed served as chief of staff of Ethiopia's defence forces for about 17 months

Yakin na Tigray daya ne cikin jerin matsalolin da ke addabar Habasha, wadda rikicin kabilanci yake son kara raba kawunan 'yan kasar.

Kafin wannan lokacin Habasha ta kasance kasar da ke taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya ya yankin gabashin Afirka da ake kira Horn of Afirka, amma yanzu ita ce ke kan gaba wajen ruruta wutar rikici da ka iya raba yankin da zaman lafiya.