Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iran na zawarcin makwabtanta Larabawa
Ministan harkokin waje na Iran Javad Zarif ya yi kira ga kasashen Larabawa masu makwabtaka da kasar da su rungumi hanyar tattaunawa a matsayin hanyar da ta rage wa kasashen kawo karshen zaman doya da manja da suka dade suna yi musamman a wannan lokaci na sauyi bayan kayen da Shugaba Trump ya samu a babban zaben Amurka.
Rashin jituwa tsakanin Iran da Amurka ya kai matakin da bai taba kai wa karkashin mulkin Mista Trump.
Kamar yadda aka san shi da burga, Javad Zarif bai sauya halayyarsa ba ma a wannan karon, domin ya rubuta wa makwabtan Iran da ba sa jituwa wasika da Larabci.
A ciki ya sanar da su cewa tun da Shugaba Trump ya sha kaye a zaben shugaban Amurka, saboda haka lokaci yayi da kasashen za su daina waiwayar wasu can su tabbatar mu su da tsaro, yana kuma cewa hadin kai ne kawai zai kawo biyan bukatun al'umomin yankin.
Sakon ministan harkokin wajen na Iran a bangare guda ya aika da shi ne ga sabuwar gwamnatin Amurka mai jiran gado - tun da Joe Biden a baya mataimakin tsohon shugaba Obama ne, wanda shi ne ya tababtar da yarjejeniyar nan ta nukiliyar Iran a 2015.
Wannan yarjejeniyar na cikin ayyukan da Barack Obama ke lafahari da ita har gobe, amma sai wanda ya gaje shi ya yi watsi da ita.
A karkashin mulkin Mista Biden, bangaren gwamnatin Iran ta masu sassaucin ra'ayi na fatan Amurka na iya dawo da yarjejeniyar, sai dai kasashe kamar Saudiyya ba za su goyi bayan haka ba.
Sakon na Mista Zarif zai kasance kuma zolaya ce ga Saudiyya wadda shugabanninta ke kallon faduwar Shugaba Trump a zabe a matsayin wata babbar koma baya.
Abin lura a nan shi ne Sarki Salman na Saudiyya da dansa Yarima mai jiran gado Muhammad, sun mika sakon taya murna ga zababben shugaban Amurka Joe Biden, amma sai can bayan da dukkan muhimman shugabanni har ma da kananansu suka mika nasu sakonnin taya murna.