Charlie Hebdo: Yadda aka datse kan malamin makaranta kan hotunan ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW)

Asalin hoton, Reuters
Kafofin watsa labaran Faransa sun rawaito cewa malamin makarantar da wani mahari ya kashe kuma ya datse kansa a wajen birnin Paris ya sha fuskantar barazana kafin kisan nasa.
An ce sunansa Samuel Paty, mai shekara 47, wanda ke koyar da tarihi da ilimin yanayi.
'Yan sanda sun ce maharin matashi ne mai shekara 18 dan asalin Chechenia.
Gabanin wannan harin, malamin makarantar ya nuna wa dalibansa wasu hotunan batanci na manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.
'Yan sanda sun kashe mutumin da ya kai wannan harin jim kadan bayan faruwar al'amarin, kuma muninsa ya sa shugaban kasar Emmanuel Macron halartar wurin.
Jim kadan bayan karfe biyar na yammacin jiya Juma'a, wani mutum dauke da wata doguwar wuka ya kai wa wani malamin tarihi hari a gaban makarantar da yake koyarwa a bayan unguwar Conflans-Saint-Honorine.
Maharin ya yi amfani da wukar wajen yanke kan malamin makarantar sannan ya tsere daga harabar makarantar, kuma ba a jima sai ya yi gaba-da-gaba da jami'an 'yan sandan birnin.
Sai dai ya ki mika wuya su kama shi, a sanadiyyar haka 'yan sanda suka harbe shi, kuma ya mutu a kan hanyar kai shi asibiti.
Kafofin yada labaran Faransa na cewa malamin makarantar ya nuna wa daliban da yake koyarwa wasu zane-zane na batanci da aka yi kan Annabi Muhammad SAW.
Hotunan na da alaka da harin da aka kai wa mujallar nan ta Charlie Hebdo da ta fara wallafa hotunan batancin a 2015.
Ilimin 'yancin fadin albarkacin baki

Asalin hoton, EPA
Munin harin ya ja hankalin shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya ziyarci wurin jim kadan bayan da harin ya auku.
"Ba zan yi magana kan ainihin abin takaicin da ya faru a nan ba da yammaci a Conflans Saint-Honorine, amma an kashe daya daga cikin 'yan kasarmu saboda yana koyarwa, saboda yana sanar da dalibai ilimin 'yancin fadin albarkacin bakinsu da kuma 'yancin yarda ko rashin yarda. Wanda ya kai ma sa wannan harin takaicin ba abin koyi ba ne kuma harin na ta'addanci ne," in ji shi.
Shugaba Macron ya yi kira ga 'yan kasar da su hada kansu wuri guda.
Wane ne mutumin da aka kashe?
A cewar jaridar Le Monde, mutumin da aka kashe, malami ne da ke koyar da tarihi da ilimin sanin yanayi, wanda yake koya wa dalibansa 'yancin fadar albarkacin baki da ke da alaka da zanen batanci da mujallar nan ta Charlie Hebdo ta yi kan Annabi Muhammad (SAW).
Rahotanni sun ce malamin ya shawarci Musulmi su fita daga ajin idan suna gani hakan zai harzuka su.
Tun farkon wannan watan wasu Musulmi kuma iyayen daliban makarantar sun kai kukansu ga hukumomin makarantar kan yadda malamin yake nuna wa dalibansa hotunan batancin a cikin ajin da yake koyarwa, a cewar kafofin watsa labaran Faransa.

Asalin hoton, AFP
Idan aka tabbatar da cewa wannan ne dalilin da aka kashe malamin makarantar, Faransawa za su girgiza matuka -- saboda a ganinsu malamin bai aikata laifin da ya wuce bayyana tarihin ainihin abin da ya auku a kasar tasu ga dalibansa ba.
Masu bincike sun tabbatar da maharin matashi ne mai shekara 18 da haihuwa kuma haifaffen kasar Rasha ne.











