Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Japan: Abin da ya sa yawan mutanen da ke kashe kansu a ƙasar ke ƙaruwa
Adadin masu kashe kansu a Japan na ci gaba da karuwa, inda a yanzu aka fi yawan samun mata masu karancin shekaru da ɗaukarwa kansu irin wannan mataki.
Kimanin mutane dubu daya da dari takwas ne suka hallaka kansu a kasar a watan Satumba kadai.
Adadin matan da ke kashe kansu ba tare da sun haura shekara ashirin ba a duniya ya ninka har sau hudu a wannan shekarar idan aka kwatanta da bara.
Hukumomi a kasar sun ce annobar korona wacce ta zama annoba ta sauya rayuwa ga matasa da yawa.
Hukumomi na ci gaba da yin kira ga matasa da su nemi shawarwarin ƙwararru a duk lokacin da suka tsinci kansu cikin damuwa maimakon ɗaukar irin wannan mataki.
An kuma samu karuwar taurari ko fitattun mutane da ke kashe kansu a kasar, abin da ke da da nuna matsin da suke sha daga al'umma.
Sai dai duk da haka an samu saukin irin wadannan rahotanni a Japan a shekarun baya bayan nan idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a can baya.