Yadda arzikin attajiran duniya ke ci gaba da dagawa a lokacin korona

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa arzikin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya ya karu da fiye da kashi daya cikin hudu a lokacin cutar korona.
Rahoton binciken wanda wani bankin Switzerland mai suna UBS ya gudanar, ya kuma gano cewa adadin masu kudi a duk duniya ya karu zuwa kasa da dubu biyu da dari biyu.
Wanda yafi kowa kudi a duniya shine Jeff Bezos - mai kamfanin Amazon - wanda aka kiyasta yana da kimanin dala biliyan dari biyu.
Wani rahoto a shekarar da ta gabata daga Oxfam ya gano cewa attajiran da suka fi kudi a duniya su ashirin da shida sun mallaki abin da ya haura na rabin talakawan duniya baki dayansu.

Asalin hoton, Getty Images
Rahoton ya alakanta karuwar arzikin attajiran da hana zirga zirga da kasashe da dama na duniya suka yi, abin da ya tilastawa jama'a komawa yin ciniki ta Internet.
Kamfanonin aikawa da sakonni sun sake farfadowa a lokacin da shagunan Internet suka zamo zabin da jama'a ke da shi domin ba bu damar fita aje kasuwa.
Osef Stadler, wata jami'a a bankin na UBS wanda ke hulda kai tsaye da masu hannu da shuni a duniya, ta ce: "Attajiran sun yi rawar gani a lokacin cutar korona".
Kasuwannin hannayen jari na duniya tun daga wannan lokacin sun sake yin kaso sosai sakamakon yawan asarar da aka tafka.
Hannayen jari a wasu kamfanonin fasaha - wanda galibi ke hannun masu kuɗi - sun yi sama sosai a cewar rahoton.











