Rikicin ƙabilanci ya zama ruwan dare a Habasha

Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Habasha ta ce ta damu matuka game da rikice-rikicen kabilanci biyu da aka samu a baya-bayan nan a yankin Benishangul Gumuz da ke yammacin kasar.

Hukumar ta yi kira ga gwamnati ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin bincikar yadda lamarin ya auku.

Wani jami'i da ke kula da tsaro a yankin ya musanta rahotannin kafofin yada labarai na cikin gida da ke cewa sama da mutane tamanin sun mutu a hare-haren.

Ya zargi jam'iyyun adawa da rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai sama da mutane miliyan daya da ke gudun hijira a cikin gida yanzu haka a kasar, bayan da suka tsere daga gidajensu sakamakon rikici.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter Firai ministan Habasha Abiy Ahmad, ya zargi kungiyoyin 'yan adawa da kokarin kawo nakasu ga abin da ya kira ''Aniyar kawo sauyi''.

Tashe-tashen hankula dai na kara kamari a kasar, ciki har da wadanda suka jibanci kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

Kazalika an sha zargin gwamnatin shugaba Abiy Ahmed da take hakkin 'yan adawa, sai dai ta sha musanta hakan.

Yawancin kasashen yamma sun yi maraba da sabbin tsare tsaren da shugaba Abiy wanda ya karbi mulki a 2018 ya bijiro da su.

Ya yi alkawarin kawo sauyi bayan kwashe gwamman shekaru ana mulkin danniya da jam'iyya guda ta yi.

Sai dai duk da ya lashe kyautar zaman lafiya a shekarar 2019 bayan kawo karshen rikici tsakanin kasarsa da makwabciyarta Eritrea, ana zargin shugaban da take hakkin 'yan adawa a cikin gida.