Chadwick Boseman: Cutar daji ta kashe tauraron fim na Black Panther

Chadwick Boseman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Chadwick Boseman ne babban jarumi a fim ɗin Black Panther
Lokacin karatu: Minti 3

Tauraron fina-finan Amurka Chadwick Boseman, wanda ya taka muhimmiyar rawa a fim din Black Panther, ya mutu sakamakon cutar daji, a cewar iyalinsa.

Tauraron mai shekara 43 ya mutu ne a gidansa da ke birnin Los Angeles kuma matarsa da 'yan uwansa suna kusa da shi lokacin da ya cika.

Boseman bai bayyana wa duniya cutar da ya yi fama da ita ba.

"Chadwick gwarzo ne wanda ya jure sosai, sannan ya fito a fina-finai da kuke matukar kauna," a cewar iyalinsa a wata sanarwa da suka fitar.

"Daga fim din Marshall zuwa Da 5 Bloods, da fim din August Wilson Ma Rainey na Black Bottom da kuma fina-finai da dama - dukkansu an dauke su yayin da yake fama da tiyata daban-daban da kuma gashin da ake yi wa masu fama da cutar daji. Abin alfahari ne a gare shi da ya taka rawa a matsayin Sarki T'Challa a fim din Black Panther."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Sunan Boseman ya fito ne a rawar da ya taka ta kwaikwayon fitattun mutane irin su Jackie Robinson a fim din 42 da aka yi a 2013 da mawaki James Brown a fim din Get on Up da aka yi a 2014.

Sai dai ya fi shahara a fim din Black Panther da aka yi a 2018.

A cikin fim din, Boseman ya taka rawa a matsayin sarkin Wakanda, wata ƙasar da aka ƙago a nahiyar Afirka da tafi sauran ƙasashen duniya ci gaba a fannin fasahar zamani.

Fim din ya burge matuka kuma ya tar wa wadanda suka yi shi fiye da dala biliyan 1.3 a gidajen silman duniya da aka haska shi.

A bara Boseman ya ce fim din ya sauya abin da duniya ke fahimta game da rayuwar "matasa bakar fata masu baiwa".

Ya kuma taka wannan rawar a wasu jerin fina-finan Marvel Comics kamr Captain America: Civil War, da Avengers: Infinity War da Avengers: Endgame.

Labarin mutuwarsa ta gigita masoyansa saboda bai taba sanar da duniya yana fama da cutar daji ba.

Amma masoyansa sun lura cewa yana ramewa kuma wasu cikinsu sun bayyana damuwarsu.

Manyan taurarun fina-finai na ta mika sakonninsu kamar Mark Rufallo:

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

1px transparent line

Manyan 'yan siyasa kamar 'yar takarar mukamin mataimakin shugaban Amurka Kamala Harris ma ba a bar su a baya ba:

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

1px transparent line

An haife shi a jihar South Caolina, mahaifiyarsa nas ce wato ma'aikaciyar jinya, mahaifinsa kuma dan kasuwa mai yin kujeru ne. Boseman ya halarci jami'ar Howard da ke Washington DC, babban birnin Amurka.

Amma sai 2013 duniya ta san shi duk da cewa ya dade yana fitowa a wasannin talabijin. A shekarar ya fito cikin fim mai suna 42.

Chadwick Boseman at the commencement address

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Boseman, a shekarar 2018 yayin wata ziyara da ya kai jami'ar Howard

A 2018 Boseman ya koma jami'ar da ya halarta domin yin jawabi ga daliban da aka yaye.

Ya ce "Wasunku sun rika yin turjiya ga jami'ar ita kanta," ga daliban da yawancinsu bakaken fata ne.

"Yawancinku za su fita daga jami'ar Howard kuma ku sami kanku a wuraren da ke nuna bambanci ga wadanda ba turawa ne ba," inji shi.

"Amma ganin cewa kun sha gwagwarmaya a cikin wannan jami'ar da ku ke kauna matuka alama ce da za ta taimaka muku amfana da ilimin da ku ka samu domin inganta rayuwar duniyar da za ku shiga yanzu".