Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara zai nemi ta-zarce a karo na uku

Asalin hoton, Getty Images
Bayan jan kafa na tsawon lokaci a yanzu ta tabbata cewa shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara zai nemi ta-zarce a wa'adin mulki na uku a zaben da zai gudana a cikin watan Oktoba.
'Yan adawa na cewa matakin ya sabawa kundin tsarin mulki kasar amma ya ce hakan bai sabawa doka ba.
Amma me ya sa Mr Outtara zai sake tsayawa takara?
Ouattara ya shafe kusan shekaru 10 yana jan ragamar kasar ta Ivory Coast, kuma a cikin watan Maris din bana ya bayyana cewa ba zai nemi ta-zarce ba.
Amma abubuwan sun sauya daga watan Yuli saboda mutumin da Ouattara yake son ya gaje shi a matsayin shugaban Ivory Coast watau Amadou Gon Coulibaly - wanda shi ne firaiministan kasar, ya rasu sakamakon bugun zuciya ana tsaka da taron majalisar ministocin kasar a watan da ya wuce.

Asalin hoton, AFP
Hakan ya cefa jam'iyya mai mulkin kasar cikin tsaka mai wuya, abin da wasu ke ganin yasa Mr Ouattara ya ce ba zai sauka ba zai nemi tazarce.
"Na yanke shawarar amsa kiran 'yan kasa, na yanke hukunci sadaukar da kai na," in ji Ouattara.
Wasu na ganin zaben na watan Oktoba a matsayin zakaran gwajin dafi saboda yakin basasan da aka yi a shekara ta 2010 lokacin da Ouattara ya lashe zabe a karon farko, lamarin da ya janyo mutuwar mutane kusan dubu uku.
Masu adawa sun ce kundin tsarin mulkin Ivory Coast ya ba shi damar yin wa'adin mulki biyu ne kawai amma shugaban kasar ya ce mulkinsa na kusan shekaru 10 baya cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar na shekara ta 2016.

Asalin hoton, Getty Images
Babbar jam'iyyar adawa ta Ivorian Popular Front (FPI) ta bayyana matakin Mr Ouattara na neman tazarce a matsayin abin kunya kuma za ta kalubalanci matakin a kotu.
Babban dan takarar jam'iyyar adawa shi ne Henri Konan Bedie - watau tsohon shugaban kasar daga shekarar 1993 zuwa 1999.
Ana tunanin zaben zai yi zafi sosai kamar irin na 2010 wanda Gbagbo yaki yarda ya sauka daga kan mulkin bayan Ouattara ya doke shi a zabe, lamarin da ya janyo rikicin siyasa da kashe-kashe a kasar.
Bedie ya ce jam'iyyarsa da ta tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo sun amince su yi aiki tare idan har aka je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar domin su kawar da Ouattara.
A ranar 31 ga watan Oktoba ne za a yi zagayen farko na zaben.
Shin wanene Alassane Ouattara ?
Alassane Ouattara ya zama shugaban kasar Ivory Coast ne a ranar 4 ga watan Disambar 2010 inda ya maye gurbin Laurent Gbagbo sannan a shekara ta 2015 aka sake zabensa domin wa'adin mulki a karo na biyu.
An haifi Alassane Dramane Ouattara a ranar 1 ga watan Junairun 1942 a garin in Dimbokro kuma dangin mahaifinsa musulmai ne 'yan Burkina Faso masu rike da sarautar gargajiya kuma a a shekarar 1972 ya samu shaidar digirin digirgir daga jam'iyyar Pennslvania ta Amurka.

Asalin hoton, AFP
Kasancewarsa masanin tattalin arziki, ya yi aiki a wurare da dama ciki da hadda hukumar bada lamuni ta duniya - IMF da kuma babban bankin kasar.
A rike mukamin Firaiministan kasar daga shekarar 1990 zuwa 1993 kafin ya zama shugaban jam'iyyar Rally of the Republicans (RDR) mai mulkin kasar a shekarar 1999.
A bangaren iyali kuwa a shekarar 1991, Shugaba Alassane Ouattara ya auri bafaranshiya Dominique Nouvian, kuma suna da 'yaya biyu.











