Drogba na takarar shugaban hukumar kwallon Ivory Coast

Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon dan wasan gaban Chelsea Didier Drogba ya gabatar da takararsa a hukumance, ta neman zama shugaban hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast.

Drogba ya tara dubban magoya baya a wajen ofishin hukumar yayin da ya je mika takardunsa a ranar Lahadi. Za a gudanar da zaben ne a watan gobe.

Yana cikin 'yan takara hudu da ke neman wannan matsayi. Duka kuma za su za a tabbatar da sun bi tsrain fitar da suna ye gabanin a sanar da dan takara na karshe.

"Kwallon kafa wasan kowa ne, kuma kwallon kafa na hada kan mutane waje guda, kwallon kafa magana ce ta hadin kai. Za kuma mu iya tabbatar da haka saboda abin da muke gani na mutanen da suka yi cuncurundo a wajen hedikwatar hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast," kamar yadda aka ruwaito yana shaida wa manema labarai.

Drogba ya godewa magoya bayansa a wani sakon Twitter da ya wallafa tare da hotunan taron magoya bayan:

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Ivory na ta fadi ta shi tun bayan nasarar da ta samu ta lashe kofin kasashen nahiyar Afrika a 2015.