Facebook, Google, Apple da Amazon za su bayyana gaban Majalisar Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Mai kamfanin Facebook zai bayyana a gaban majalisar Amurka ta intanet domin ya gaya wa hukumomin kasar su sabunta dokokin da ake tafiyar da tsarin na intanet.
Mark Zuckerberg tare da wasu shugabannnin manyan kamfanonin fasahar zamani za su bayyana a gaban wani kwamitin majalisar da ke son duba yadda ayyukan manyan kamfanonin ke shafar kananan kamfanonin fasaha da ke fafata wa da su a fagen kasuwanci.
Ana kuma sa ran zai yi kira ga gwamnatoci su kara sa ido kan ayyukan manyan kamfanoni irin nasa.
Matakin da Mista Zuckerberg ke son dauka sabo ne - ana iya cewa wa ma babu kamfanin da ya taba daukar irinsa a tarihin duniya.
A yau Laraba, kamfanoni hudu mafi girma a fagen fasahar zamani za su bayar da bahasi ga mambobin majalisar Amurka.
Mark Zuckerberg na Facebook da Sundar Pichai na Google, da Tim Cook na Apple da kuma Jeff Bezos na Amazon za su sha tambayoyi daga yan majalisar.
Jeff Bezos wanda shi ne attaijirin da yafi kowa kudi a duniya bai taba bayyana a gaban majalisar kasar ba. Kuma ba a taba yi wa shugabannin wadannan kamfanonin tambayoyi a lokaci guda ba a tarihin duniya.

Asalin hoton, Reuters
Saboda haka kowa zai sa ido ya ga abin da shugabannin kamfanonin za su ce da abin da za su yi - domin daga yau dangantakarsu da gwamnatin Amurka na iya sauyawa - sauyawar da babu wanda ya san inda abubuwa za su nufa.
Abu mafi muhimmanci da gwamnatin Amurkar za ta so sani shi ne ko kamfanonin sun yi girma da karfin da ya wuce kima.
Anobar Covid-19 ta kware dukkan wani mayafi da a baya ke boye gaskiyar lamarin. Domin ba kamar yadda wasu kamfanoni suka rika gazawa ba, manyan kamfanonin fasahar zamanin sai kara bunkasa suke yi.
Idan aka auna, darajar wadannan kamfanonin hudu ta zarce dala tiriliyan biyar. Wannan ne yasa ake cewa sun yi girman da babu yadda za a iya bari su gaza.
Kuma akwai jerin korafe-korafe da ke kara bayyana kan yadda suke gudanar da harkokinsu na kasuwanci.

Asalin hoton, Getty Images
Babban abin damuwa shi ne kamfanonin sun mallaki wasu bangaori na intanet - kuma ana ganin suna amfani da karfinsu wajen korar kananan kamfanoni daga kasuwa.
Ga misali - Amzon kan fifita kayan da yake samarwa a kasuwar da shi kansa ya kafa kuma yake gudanawarwa da kansa.
Ko kuma yadda Apple ke tilastawa masu manhaja a kasuwarsa ta App Store su biya shi kashi talatin cikin dari na dukkan cinikin da suka yi.
Ko kuma yadda Google da Apple ke sarrafa fasahar Android da ta iOS - manhajojin da ke tafiyar da ilahirin wayoyin hannu na duniya, wanda ya basu karfin korar wanda suka ga dama daga kasuwa - inda babu mai sa ido a kan harkokinsu ya tabbatar ko sun yi adalci ko ba su yi ba.

Asalin hoton, AFP
Akwai kuma wata muguwar halayya kamfanonin na sayen dukkan kamfanin da suke fargabar zai iya yin zarra a kansu, amma mai makon su raya shi, sai su kashe kamfanin bayan sun tatse shi.
Babu shakka akwai batutuwa masu yawa da ke gaban majalisar ta Amurka, kuma babu shakka kamfanonin za su fuskanci sauye-sauye musamman ganin yadda dangantaka tayi tsami tsakanin wasunsu da gwamnatin da Donald Trump ke jagoranta.











