Rabiot zai maye gurbin Pogba, Man Utd na son rike Ighalo

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United tana son karbo dan wasan Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 25, a yarjejeniyar musayar da za ta yi da Juventus don bayar da Paul Pogba, mai shekara 27. (Calciomercato - via Express)
A gefe guda, Manchester United tana ci gaba da tattaunawa da Shanghai Shenhua game da tsawaita zaman aron dan wasan Najeriya Odion Ighalo zuwa watan Janairu na 2021. (Goal)
Tsohon dan wasan Manchester United Dimitar Berbatov ya bai wa kungiyar shawarar kada ta dauko dan dan wasan Bayern Munich dan kasar Brazil Philippe Coutinho a bazarar da muke ciki. (Mirror)
Fatan dan wasan Arsenal dan kasar Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, na komawa Boca Juniors yana neman gushewa saboda rashin tabbas kan makomarsa. (Fox Sports Argentina, via Evening Standard)
Manchester United tana ci daga da samun kwarin gwiwar cewa za ta dauko dan wasan gaba Jadon Sancho, mai shekara 20, kafin kakar wasa mai zuwa duk da yunkurin Borussia Dortmund na sabunta kwangilar dan wasan na Ingila. (90min)
Stoke City da Preston North End suna cikin shirin ko-ta-kwana bayan Celtic ta gaza sabunta kwangilar dan wasanta mai shekara 32 Jonny Hayes. (Mail)






