Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus ta shiga kauyukan jihar Kaduna - El Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna damuwa kan karuwar masu dauke da cutar korona a wasu kauyukan jihar.
A cewarsa mutanen da suka kamu da cutar a yankunan karkara, sun shiga shigar ce ta barauniyar hanya, kuma a yanzu haka ana yada cuta sosai a tsakanin al'umma.
Sanarwar da kakakinsa, Muyiwa Adekeye ya fitar, ta ce an samu masu dauke da cutar a kananan hukumomi bakwai na jihar ciki hadda - Giwa da Igabi da Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu da Makarfi da Soba da kuma Zariya.
Sanarwar ta kara da cewa mutum hudu da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar - NCDC ta ce na dauke da cutar korona, sun shiga jihar ne daga wasu jihohin kasar.
A ranar Juma'a gwamna El Rufai ya yi rangadi zuwa wasu manyan hanyoyin da ake shiga jihar domin gani da idonsa da kuma kokarin hana shiga jihar da mutane daga wasu jihohin kasar ke yi.
Hukumomi a Najeriya sun haramta zirga-zirga tsakanin jihohin kasar domin dakile yaduwar cutar korona kasar.
Masu ayyuka na musamman ne kadai ke da izinin yin balaguro a wannan lokacin da ake amfani da dokar kulle a sassan kasar da dama.