Shin 'yan Najeriya sun ga amfanin rufe kan iyakokin kasar?

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan kasar sun ga irin amfani da rufe iyakokin kasar ya yi a fannin tattalin arzikinta.

Malam Garba Shehu, kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shaida wa BBC hakan, ya jaddada cewa ba za a bude iyakokin kasar ba sai gwamnati ta samu tabbaci daga wurin makwabtanta cewa ba za a su rika yin abubuwan da suka saba wa doka ba a kan iyakokin.

Ya yi tsokacin ne a yayin da Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta aiki da shawarar wani kwamitin bangare uku da ya kunshi Najeriya da Benin da Jamhuriyar Nijar game da rufe iyakokin kasar na tudu da gwamnatinsa ta yi.

Ya ce da zarar kwamitin ya kammala aikinsa kuma ya mika wa Nijeriya rahoto, gwamnatinsa za ta duba wannan batu.

Malam Garba Shehu ya ce gwamnati na jiran abin da rahoton zai gabatar kafin daukar mataki na gaba.

A cewarsa akwai miyagun halaye da ake gudanarwa ta amfani da makwabtan kasashen da suka hada da fasakwauri da kuma safarar miyagun kwayoyi da makamai.

Mai bayar da shawarar ya ce Najeriya ta ga dimbin alfanun rufe kan iyakokin, musamman irin bunkasar tattalin arzikin da lamarin ya kawo wa kasar masu noman shinkafa.

Ya ce abin alfahari ne ganin yadda 'yan kasar suka fahimci cewa za su iya noma abincin da za su ci har su sayar cikin sauki.

Sama da wata shida ke nan da gwamnatin Nijeriya ta rufe iyakokinta da nufin shawo kan matsalar fasa-kwaurin shinkafa da sauran haramtattun kayayyaki.