Shugabannin majalisun dokokin Najeriya na so a kare su daga tuhuma

'Yan majalisa na so shugabanninsu su samu kariya kamar yadda shugaban kasa da gwamnoni ke samu

Asalin hoton, Lawan/Femi Twitter

Bayanan hoto, 'Yan majalisa na so shugabanninsu su samu kariya kamar yadda shugaban kasa da gwamnoni ke samu

Kudurin dokar bayar da ke neman bayar da kariya ga shugabannin majalisun tarayya a Najeriya ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilan kasar.

Dokar na neman ganin shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa da takwarorinsu na majalisar dattawa sun amfana da dokar da za ta kare su daga fuskantar shari'a a lokacin da suke rike da madafun iko.

Yunkurin 'yan majalisar na yi wa dokar kariya ta kasar gyaran fuska ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan kasar har ma da wasu 'yan majalisar game da dacewa ko rashin alfanun dokar.

A baya dai tanadin dokar kariya da ke sashe 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya kebance shugaban kasa da gwamnoni da mataimakansu ne kadai.

Wani dan majalisar wakilai, Sada Soli, ya shaida wa BBC cewa dokokin majalisa sun riga sun bayar da kariya ga shugabannin majalisa domin su fadi ko su yi abin da suke a cikin majalisa ba tare da sun fuskanci hukunci ba.

''Duk abin da muke yi idan dai a cikin dandalin majalisa ne, kai ba ma cikin dandalin majalisa ba, idan muna cikin farfajiyar majalisa, duk abin da dan majalisa yake so ya yi ba ma shugabanta ba, zai iya yi.

''Yana iya yi, yana da wannan damar kuma idan ya fito ba a iya ce masa komai,'' a cewarsa.

Amma masu ganin dacewar samar da dokar irin su Mustapha Aliyu na cewa yin hakan zai bai wa shugabannin majalisar damar mayar da hankali wurin gudanar da ayyukansu ba tare da tsaiko saboda wani zargi ko fuskantar shari'a ba.

Ya ce muhimmiyar rawar da majalisar kasar za ta taka wajen yaki da rashawa na bukatar samun irin wannan kariya, ''Idan shugabannin majalisar ba su da kariyar da za ta sa su iya jagoranci a aikin da ya kamata a yi ga kawo nasara to akwai matsala.''

Ya kuma ce dokokin majalisar da ke ba da kariya ga dukkan 'yan majalisa, dokokin na cikin gida ne da suka kebanci majalisar.

''Dokoki ne da suka shafi zauren majalisa...kowanne dan majalisa yana da wannan kariya", in ji shi.

Kungiyar da ke bibiyar ayyukan 'yan majalisan kasar, CISLAC, na ganin akwai wasu ayyuka da ya kamata 'yan majalisar su fi mayar da hankali a kansu ba batun bai wa shugabanninsu kariya ba.

''Kullum hari ake kai wa mutane a Najeriya, 'yan majlisar nan basu fito sun yi batu a kan cewa duk wanda ya saci dukiyar kasa sun yi bara'a da shi ba,'' a cewar shugaban kungiyar Awwal Musa Rafsanjani.

Ya kara da cewa bai kamata matsayin mutum ta hana a bincike shi ba.

''A kasashen da ake dimokradiyya da inda aka ci gaba, ko da kai shugaban kasa ne, idan ka yi ba daidai ba to wannan ba zai hana a bincike ka ba. Kwanan nan shugaban Amurka da ake zargi da wasu laifuka ai an bincike shi", a cewarsa.

Rafsanjani ya ce ba kyakkyawan wakilci ba ne ko aikin majalisar a ce, ''Ka zo ka ce za ka yi doka don ka kare kanka daga ba da bayanai ko kuma ka yi doka domin kar a tuhume ka da irin barnar da kake sha'awar yi.''

Ko da sabon kudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisun tarayyar kasar, sai an fara mika ta ga majalisun dokokin jiha 36 na kasar domin mahawara da amincewa.

Daga nan kuma za a yi mahawarar jin ra'ayoyin 'yan kasar a game da hakan, kafin shugaban kasar ya sanya hannun ta zama doka.