Girgizar kasa: Mutum 8 sun mutu a Turkiyya, wasu sun jikkata a Iran

A kalla mutum 8 girgizar kasa ta kashe, cikinsu har da kananan yara uku, a gabashin Turkiya mai makwabtaka da Iran.

Ministan harkokin cikin gidan Turkiyya Suleyman Soylu ya ce girgizar kasar ta jikkata wasu mutum 21 tare da rusa gini dubu daya da shida a Turkiyya.

A kasar Iran inda girgizar ta taso kuma, mutum fiye da 40 ne suka samu raunuka baya ga gidajen da suka rushe a kauyukan lardin yammacin Azerbaijan.

Kafafen yada labaran Turkiyya sun yada bidiyon yadda masu aikin ceto ke hako wurare domin zakulo mutanen da suka makale a karkashin gini, yayin da iyalai ke jira a cikin dusar kankara a lardin Baskale na jihar Van.

"Akwai kananan yara da suka makale a cikin baraguzan gini. Mun ji muryoyinsu.

"Daga nan sai wani abin da ba mu gane ba ya faru, amma dai mun zakulo gawa uku,'' inji wani mazaunin kauyen.

Amma gwamnan Van Mehmet Emin Bilmez ya ce babu sauran wasu mutanen da suka makale a karkashin gini.

A watan Janairu iftila'in zaftarewar kankara ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 39, cikinsu har da masu aikin ceto.

Wasu mutum 31 kuma suka mutu a yankunan Elazig da Malatya baya ga mutum 1,600 da suka samu rauni a wata girgizar kasa.

Ana yawan samun girgizar kasa a yankin.

A shekarar 1999, mutum kusan 17,000 sun mutu a wata girgizar kasa a birnin Izmit da ke yammacin Tukiyya.

A Iran kuma, girgizar kasa mafi muni a tarihin kasar ita ce ta 1990 wadda ta kashe 40,000 tare da raba wasu miliyan daya da muhallansu.