Hotunan yadda Zulum ya raba kayan abinci a Nijar

Wasu daga cikin kayayyakin da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kai wa 'yan gudun hijira a jihar Diffa ta jamhuriyar Nijar.

Kusan 'yan gudun hijira dubu 30 ne suka amfana da kayayyakin taimako da gwamna Zulum ya kai.

Yayin raba wadannan kayayyaki, har sai da kusan mutum 20 suka rasa rayukansu wasu 12 kuma suka ji rauni yayin turmutsutsu wajen amsar taimakon.

Wata majiya ta kusa da asibitin Diffa ta ambato mutum 20 mafiya yawan su mata da yara da kuma tsofafi ne wannan lamari ya rutsa da su.

Farfesa Zulum da kansa ya sa ido yayin da ake rabon kayayyakin abinci.

Farfesa Babagana Umara Zulum tare da gwamnan jihar Diffa Malam Issa Lamine.

Dandazon mutane sun fito domin nuna jin dadinsu yayin ziyarar da Farfesa Zulum ya kai a jihar ta Diffa.