Sudan ta Kudu: Riek Machar ya yi watsi da bukatar Kiir kan jihohi

Tsohon madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar, ya bayyana damuwa a kan tayin da Shigaba Salva Kiir ya yi domin bayar da damar kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar.

A ranar Asabar ne shugaban kasar Salva Kiir ya amince da bukatar 'yan adawa ta rage yawan jihohin kasar.

Shugaban ya kuma sallami kashi biyu bisa ukun gwamnonin jihohin kasar domin samun damar takaita yawan jihohin zuwa goma.

Amma Riek Machar ta wata sanarwa da ya fitar, ya yi watsi da bukatar da shugaban kasar ya mika ta neman kafa karin shiyyoyin mulki uku a kasar.

Rahotanni daga kasar na cewa har yanzu ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin Shugaba Salva Kiir da Riek Machar - jagoran 'yan tawaye a yakin basasar kasar na shekara biyar.