Amurka za ta mayar wa Nigeria $300m cikin kudin da Abacha ya sace

Gwamnatin Amurka ta ce za ta mayar wa Najeriya karin sama da $300m da tsohon shugaban mulkin sojin kasar marigayi Janar Sani Abacha ya sace.

Amurkar ta ce an yi safarar kudin ne a lokaci da kuma bayan mulkin Janar Abacha, wanda ya rasu a shekarar 1998.

Gwamnatin Birtaniya ce ta kwace kudin da aka boye a tsibirin Jersey bayan shari'ar da aka yi ta yi kan batun - ciki har da kalubalantar Amurka a shekarar 2014.

Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce marigayi Abacha da 'yan korensa sun wawure dukiyar 'yan Najeriya, tare da karya dokokin kasa da kasa ta hanyar boye kudaden.

Ma'aikatar ta ce tana kokarin sake gano wasu karin kudaden Najeriyar da aka sace.

A ranar Laraba ne aka fitar da wata sanarwa bayan taron majalisar ministocin Najeriya inda gwamnatin ta ce a shirye take ta gano $321m da Abacha ya wawure.

Ta kuma ce za ta kwace wasu kadarori na tsohon gwamna James Ibori da tsohuwar ministar albarkatun mai Diezani Alison Madueke.

Cikin Disambar 2017 ne Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimta da Switzerland kan maido da makudan kudade da suka kai $322m wanda tsohon shugaban kasar ya yi sama-da-fadi da su.

Wasu rahotannin sun ce an yi amfani da kudaden wajen tafiyar da shirin agazawa marasa galihu da aka fara cikin Disambar 2016.

Ko a shekarar 2018, mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen taimaka wa marasa karfi ta hanyar ba su naira dubu biyar-biyar duk wata.