Coronavirus: China ta amsa gazawa

Za a fara tilastawa jama'a rufe baki da hanci da nufin rage bazuwar cutar Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a fara tilastawa jama'a rufe baki da hanci da nufin rage bazuwar cutar Coronavirus

A karon farko gwamnatin China ta amsa cewa an yi sanyin jiki wajen tunkarar cutar Coronavirus.

Haka ma ta bayyana cewa an samu kalubalen da ya kawo tsaiko wajen tunkarar cutar.

Kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa ya ce babu makawa dole ne hukumar agajin gaggawa ta shawo kan yaduwar wannan cuta ta Coronavirus.

Kuma tuni an fara ganin sauyi, inda aka shiga kargame duk wata kasuwa da ake sayar da dabbobin da ake zargin daga can ne wannan cuta mai hana numfashi ta bulla.

Kawo yanzu mutane 20,000 sun kamu yayin da 425 su ka mutu.

Bincike ya nuna cewa mutun 3,000 ne ke kamuwa da Coronavirus a duk rana.

Kuma tuni adadin wadanda suka mutu ya zarta na cutar Sars wadda akayi a shekarar 2003.

An samu kamuwar mutun 150 a wajen Chana tare da mutuwar mutun daya a Philippines.
Bayanan hoto, An samu kamuwar mutun 150 a wajen Chana tare da mutuwar mutun daya a Philippines.

Rahotanni sun kuma nuna cewa ko a wajen China wadanda suka kamu da cutar sun kai mutun 150 tare da rahoton mutuwa daya a Philippines.

Coronavirus na farawa ne da zazzabi daga nan kuma sai tari wanda daga karshe zai kai me fama da ita kwance.

Wannan annoba ta yi sanadiyyar mummunar faduwar hannayen jarin China a ranar Litinin, wanda ba a ta taba gani ba a cikin shekara hudu.

Gwamnatin China haka ma ta zargi Amurka da tsoratar da al'umma da kuma kai lamarin inda bai kai ba.

Yanzu dai hukumomi sun soma tilastawa yankunan da ke da yawan jama'a miliyan 300 saka kyallen rufe baki da hanci, yayin da ake ta fadi tashin neman maganin cutar ta Coronavirus.