Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An samu raguwar haihuwa a China
An samu gagarumar raguwar haihuwa cikin shekaru 70 da mulkin kwamunisanci ke jagorantar kasar China, duk da raguwar sukar tsarin haihuwar Da fiye da daya da aka yi a kasar.
Wata kididdiga ta nuna a shekarar 2019, an samu raguwar da kashi 10 da digo 48 cikin mutane 1,000, raguwa mafi karanta da aka samu a tarihi tun shekarar 1949.
Har wa yau, baki daya shekarar da ta wuce an haifi jarirai 580,000, amma a shekarun baya an haifi sama da jarirai miliyan 14.
A shekarar 1979 gwamnatin China ta kafa wata doka ta tsarin haifar Da daya ga ma'aurata da nufin rage yawan al'ummar da ta ke fama da shi.
Duk iyalai ko ma'auratan da suka karya wannan doka, gwamnati na cinsu tara, wasu kan rasa aikin su baki daya a wasu lokutan kuma ana tirsasa mata zubar da cikin.
Wannan tsari dai ya fuskanci suka daga sassa daban-daban na kasar, daga bisani kuma aka fara dora alhakin tsarin na gwamnati da shi ya janyo rata tsakanin mata da maza da kididdigar shekarar da ta gabata ta nuna maza sun fi matan China yawa da miliyan 30.
A shekarar 2015 ne gwamnati ta kawo karshen tsarin haihuwa Da daya tilo ga ma'aurata, inda aka amince da haihuwar 'ya'ya biyu ga wadanda ba su taba haihuwa ba.
Shekara da shekaru kenan China ke fuskantar raguwar haihuwa, wanda hakan babbar barazana ce ga kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Wani abu na daban a China, shi ne baya ga raguwar haihuwar da aka samu, an kuma samu raguwar mace-mace a kasar mai yawan al'umma biliyan daya da miliyan hudu kamar yadda kididdiga ta nuna a bara.
Sai dai hukumomi da al'ummar kasar na nuna damuwa matuka kan rashin haihuwa, inda ake fargabar ma'aikata kalilan masu kankantar shekaru za su fara dawainiyar kula da tsofaffi wadanda suka yi ritaya masu yawan gaske.
Binciken da aka gudanar a shekarar 2017, ya nuna duk da fargabar da ake yi ta raguwar haihuwa a kasar Amurka da ake mata 1,000 ke haifar jarirai 12, lamarin bai kai na China muni ba, amma kuma kasar gaba ta ke da Japan da mata 1,000 ke haifar jarirai 8.
A shekarar da ta gabata haihuwa a Birtaniya da Wales ta kai kashi 11 da digo 6, idan aka kwatanta da binciken 2018 a yankin Scotlanda da Arewacin Ireland da aka samu kashi 12 da digo cikin daya.
Kididdigar bankin duniya ta shekarar 2017 ta nuna cewa yawan haihuwa a fadin duniya ya kai kashi 18 da digo 65.