Alkawurra 14 da Buhari ya yi wa 'yan Najeriya a 2020

A sakon shiga sabuwar shekarar 2020 da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta gidan talbijin din kasar, ya lissafo manyan ayyukan da yake sa ran zai yi a shekarar.

Muhimman ayyukan da shugaban ya ce zai yi a sabuwar shekarar sun hada da:

  • Tituna 47 da za a yi a tsakanin 2020/21 da suka hada da hanyoyin da suka dangana ga tashoshin ruwa.
  • Inganta jami'an tsaro ta hanyar sama musu kayan aiki na zamani da bai wa sojojin horo.
  • Manyan gadoji musamman gadar Second Niger Bridge.
  • Kammala ayyukan rukunin gidaje 13 karkashin tsarin samar da gidaje na kasa.
  • Kaddamar da filayen jirgin sama a Lagos da Kano da Maiduguri da Enugu a 2020.
  • Kaddamar da shirin aikin gona a karkara a kananan hukumomi 700 a tsawon shekaru uku.
  • Horas da ma'aikata 50,000 domin taimaka wa malaman gona 7,000 da ake da su.
  • Kaddamar da shirin gandun kiwon dabbobi a Gombe.
  • Kaddamar da titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Warri a watanni ukun farkon 2020.
  • Fara aikin hanyar jirgin kasa da za ta tashi daga Ibadan zuwa Abuja da kuma Kano zuwa Kaduna a farkon watannin ukun 2020.
  • Kara sakar wa harkar wutar lantarki mara domin bai wa masu sanya hannun jari damar samo da sayar da wutar lantarki.
  • Gwamnatin tarayya za ta horas da malaman gona 50,000 wadanda za su zama kari ga 7,000 da ake da su a kasa.
  • Fara aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mambilla a watannin shidan farkon 2020.
  • Fara aikin jan bututun iskar gas AKK gas pipeline, da OB3 gas pipeline da kuma fadada bututun iskar gas din na Escravos zuwa Lagos a watanni ukun farko na 2020.