'Yan daudu sun yi sallar dare raka'a 40 a hannun 'yan Hisbah

Abdullahi ganduje na son kakkabe alfasha daga Kano

Asalin hoton, HISBAH

Hukuma Hisbah ta jahar Kano ta kama wasu matasa su 30 da take zargin 'yan daudune, a yayin wani bikin qawa da suka shirya yi a kano.

Hukumar ta kuma saki 'yan daudun ranar Talata bayan mutanen sun yi sallar dare raka'a 40.

Da yake yi wa BBC karin haske Darakta janar na hukumar ta Hisbah Dakta Aliyu Musa Kibiya, ya ce bayan kama su sun sa su yin sallah har raka'a 40 a wani mataki na wayar musu da kai.

Latsa wannan alamar lasifikar domin sauraron Dakta Aliyu Musa Kibiya.

Bayanan sautiDakta Aliyu Musa Kibiya

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya shaida wa BBC cewa ya zo halartar bikin wani abokinsa ne. Ya ce wanda ya gayyace shi ya tsere a lokacin da 'yan Hisbah suka isa wurin.

"Sun yi mana wa'azi kuma tun da daga lokacin da suka tsare mu muna yin Sallah. Na yi nadamar abin da ya faru, kuma idan Allah Ya yarda ba zan maimaita ba," inji shi.

Mataimakin kwamandan hukumar, Tasiu Ishaq ya ce jami'an hukumar sun kama 'yan daudun ne sanye da kayan mata.

Jami'in ya ce "Abin kunya ne a ga matasa maza da irin wannan dabi'a ta yin abubuwa kamar mata."

Jihar Kano na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke aiwatar da Shari'ar Musulunci tun a shekarar 2001.