Amr Imam: Yadda gwamnatin Masar ke kama masu bijire ma ta

Hukumomi a Masar sun kama wani fitaccen lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, kwana guda byan ya ce zai fara yajin cin abinci saboda yadda ake cin zarafin lauyoyi da masu fafutukar kare hakkin bil Adama a kasar.

Rahotanni na cewa Amr Imam ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa jami'an tsaro sun isa gidansa domin kama shi.

Amr Imam na aikin kare wadanda ake tsare da su a kurkuku ne bayan da aka kama su suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da Shugaba al-Sisi a watan jiya.

Kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil Adama sun ce an kama kusan mutum 3,000 tun da aka fara boren, ko da yake an sako wasu daga baya.

Cikin wadanda aka kama akwai wasu fitattun masu fafutukar kare hakkin dan Adam, wadanda ke da alaka da juyin juya hali na shekarar 2011, ko da yake ba su shiga zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan ba.

Amma masu sukar gwamnatin Masar na cewa tana son tsorata mutane ne domin kaucewa yaduwar boren.