Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sanata Ali Ndume: Sojojin Najeriya na bukatar jiragen yaki
Kwamitin majalisar dattawan Najeriya kasar a kan sojojin kasa ya ce akwai bukatar a samar wa sojojin kasa da ke yaki da Boko Haram jiragen yaki masu saukar ungulu don kawo karshen yakin cikin sauri.
Kazalika `yan kwamitin sun bayyana cewa sojojin na bukatar kayan damara da Karin kudi da alawus don gudanar da ayyukansu.
Sanata Muhammad Ali Ndume shi ne shugaban kwamitin kuma ya shaidawa BBC cewa sun kai wata ziyara shiyyar arewa maso gabashin kasar inda ake arangama da mayakan Boko Haram.
''Ya kamata a kara yawan sojojin da ke yaki da 'yan Boko Haram, saboda sojojin da ke kasa a wajen ba su wuce 30,000 ba kuma adadin bai isa ba.
Sannan kudin da ake warewa kan sojojin a kasafin kudin Najeriya ba ya wadatarwa, saboda duka a shekarar nan an ware musu Biliyan 100 ne kadai a wannan aiki.
Dan haka fadar shugaban kasa ta sake duba lamarin a kara yawan kudin''.
Ndume ya ce sojojin sun yi alkawarin matukar aka ba su jiragen yaki masu saukar ungulu guda 10, za su iya murkushe masu tada kayar baya na Boko Haram cikin watanni uku.
Rikicin Boko Haram musamman a arewa maso gabashin Najeriya ya janyo asarar rayuka da dukiya, ya yin da ake korafin rashin kayan aiki da kyakkyawan albashi na daga cikin matsalolin da sojojin da ke wannan yaki ke fuskanta a kokarin murkushe 'yan tada kayar bayan.