Bankin Duniya: Tattalin arzikin Afirka na tafiyar hawainiya saboda bashi da rashin tsaro

Asalin hoton, Getty Images
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka zai bunkasa da kashi 2.6 cikin dari a 2019 sabanin hasashen bankin tun a farkon watan Afrilu cewa tattalin arzikin yankin na Afirka zai daga da kashi 2.8.
Bankin Duniyar ya bayyana haka ne a rahoton da ya gabatar inda a ciki ya ce 'al'amura a Afirka za su ci gaba da kasancewa cikin matsi da rashin tabbas duk da ci gaban da aka samu a wasu sassan sakamakon karancin zuba jari da rashin tabbas ga manufofin tattalin arzikin duniya.
Bankin dai ya rage hasashen bunkasar tattalin arzikin kasashen Afrika daga shekarar 2019 zuwa 2021 da kasa da kashi daya cikin dari, ba yadda ya yi hasashe ba tun farko.
Sai dai bankin ya ce sauran kasashen yankin kudu da hamadar Sahara ma ana sa ran za su samu bunkasar tattalin arziki da kashi 4 cikin dari maimakon kashi 4.7 kamar yadda aka yi tsammani a watan Afrilu.
A cewar Bankin, rikicin kasuwanci tsakanin China da Amurka, kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, da ya janyo kakaba sabbin haraji kan kayayyakinsu na daga cikin sanadin da ya haddasa wannan koma baya ga Afirka.
Rahoton ya nuna cewa rikicin kasuwancin da raguwar bunkasar tattalin arzikin duniya da faduwar farashin kayayyaki ne ke kara haifar da tafiyar hawainiya ga al'amuran kawo sauyi a kasashen na Afrika.
A cewar bankin duniyar, matsalar fari da barazanar rashin tsaro da karuwar tsadar basukan gwamnati da 'yan kasuwa masu zuba jari na kara yin barazana ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar ta Afirka.
Kasashen Najeriya da Afrika ta Kudu da Angola da ke da kashi 60 cikin dari na tattalin arzikin nahiyar duk shekara, suna fuskantar kalubale.
Sai dai wani masanin tattalin arziki a Najeriya, Abdussalam Muhammad Kani ya danganta wannan hasashe na Bankin Duniyar da yadda manyan kasashen Afirka suke fama da matsalar tsaro da tarin bashi da gwamnatoci ke ciyowa.
Ya ce kasashen Najeriya da Africa ta Kudu da Angola sune suke samar da kashi 60 cikin dari na tattalin arzikin da ake da shi a nahiyar Afirka wanda idan har tattalin arzikin wadannan kasashen ya tabu, to sauran kasashen yankin Afirka ma za su girgiza.

Asalin hoton, THETRENTONLINE
A cewar shi, mafi yawan kayayyakin da ake amfani da su a nahiyar Afirka ana shiga da su ne daga wasu kasashen wanda ya ce akwai bukatar kasashen Afirka su tashi tsaye wajen bunkasa masana'antunsu domin su iya dogaro da kansu.
Ya ce: ''Idan ka tsallaka ka shigo da kaya daga wani waje, abubuwa biyu ne ke faruwa, waccan kasar ka samar mata ayyukan yi, kasar data shigo da kayan kuma ta jefa kanta cikin matsalar rashin aikin yi.'' in ji Abdussalam Kani.
Masanin tattalin arzikin ya ce matukar shugabannin Afirka suka gaza daukar matakan da suka kamata, rashin aikin yi da talauci za su ci gaba da karuwa a nahiyar.











