Borno ta bai wa malamai 30 a Saudiyya kwangilar addu’a kan Boko Haram

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa wasu 'yan Najeriya mazauna Makkah su 30 kwangilar yin addu'o'i da kuma dawafi a kullum domin rokon Allah (SWA) ya dawo da zaman lafiya jihar Borno da kuma Najeriya baki daya.

Mutane 30 din da aka basu kwangilar wadanda suka fito daga Borno da Katsina da Zamfara da Kano da kuma wasu sassa na yankin arewa maso yammacin Najeriya, tuni dama mazauna Saudiyya ne fiye da shekaru 10 inda a kullum suke ziyartar ka'aba domin addu'o'i.

Cikin mutanen, harda wani tsoho da ya shekara 40 kullum yana Ka'aba domin gudanar da addu'o'i.

Dakin Ka'aba ne wuri mafi tsarki ga musulmai wanda dakin na nan a cikin masallacin Makkah.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Malam Isa Gusau ya bayyana cewa wannan yunkurin da gwamnan ya yi, na daya daga cikin abubuwan da ake kokarin yi na samar da tsaro da suka hada da taimaka wa sojojin Najeriya da kuma daukar 'yan sa kai da kuma mafarauta da samar musu da makamai da kuma sauran tsare-tsare na samar da aikin yi da ci gaba.

A lokacin da gwamnan jihar ya gana da malaman da ke Saudiyya a ranar Juma'a, ya yi godiya matuka a garesu inda ya nemi su ci gaba da gudanar da addu'o'i, inji Malam Isa.

Har yanzu dai ana samun hare-haren kungiyar Boko Haram a jihar Borno da sauran yankuna na arewa maso gabashin Najeriya.

Ko a makon da ya gabata sai dai aka kai hari a garin Gubio da ke jihar Borno duk da cewa sojoji sun ce sun dakile harin.

Samar da tsaro na daya daga cikin manyan alkawura uku da shugaban kasar ya yi tun a yakin neman zabensa na 2015 da kuma 2019.

Sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da tsaro a kasar sakamakon kara fadadar matsalar a wasu yankuna musamman arewa maso yammacin kasar.