Robert Mugabe: Zimbabwe da wasu kasashen na zaman makoki

Marigayi Robert Mugabe

Asalin hoton, FAIRFAX / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Marigayi Robert Mugabe

Shugaba Emerson Mnangagwa ya karrama tsohon Shugaba Robert Mugabe ta hanyar ayyana kwanakin makoki a fadin kasar.

Mista Mugabe ne shugaban kasa na farko da aka taba zaba tun da ta sami 'yancin kai.

Ya kuma ba mutumin da ya gada din lambar yabo mafi daraja a kasar.

Shugaba Emerson Mnangagwa ya fi kowa sanin Robert Mugabe.

Yanzu kuma aikin jagorantar kasar Zimbabwe a wanann lokacin zaman makoki ya hau kansa.

A man stands next to a mural of Robert Mugabe

Asalin hoton, EPA

Ya bayyana marigayi Robert Mugabe a matsayin wani gwarzo na wannan karni da muke ciki.

Wasu sun amince da wannan karramawar da aka yi wa tsohon shugaban kasar, amma wasu kuwa na nuni da yadda ya murde zabukan shugabn kasa da yadda aka rika murkushe masu adawa da mulkinsa a matsayin wata alama ta gazawarsa.

Amma duk da bambancin ra'ayi, an shirya dawo da gawarsa gida Zimbabwe kafin kwanakin zaman makokin su kare.

Kuma yadda wasu ke matukar son sa, haka wasu ke nuna tsananin kiyayya a gareshi.

Wannan yayi kama da abin da Hausawa kan ce ne: ba a guzurin masoya da makiya - duk inda ka je suna nan.