Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Sasantawa da 'yan bindigar Zamfara na tasiri'
Rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta bakin kakakinta SP Muhammad Shehu ta shaida wa BBC cewa ya zuwa yanzu masu satar jama'a don karbar kudin fansa sun sako mutane da dama sakamakon zaman sasantawar.
Ya ce a bisa yarjejeniyar wadda Kwamishinan 'yan sandan jihar Usman Nagoggo da hadin guiwar gwamnatin jihar suka shirya, 'yan kungiyar sa-kai sun saki Fulani 25 da suka kama.
Ya ce Kwamishinan ne da kansa ya je har garin Dansadau ya karbi mutanen ya je ya damka su ga gwamnan jihar.
Kwana daya bayan wannan kuma aka karbo wasu mutanen su 15, wadanda su kuma Hausawa ne a garin Shinkafi, in ji kakakin.
Haka kuma a wani daji da ke garin Gidan Dawa wanda ke karamar hukumar Kauran Namoda, da kuma wani a garin Kamarawa shi kuma a karamar hukumar Shinkafi, an karbo mutane 11, kamar yadda rundunar 'yan sandan ta bayyana.
A bayanin da kakakin ya yi wa BBC ya ce dukkanin wadannan mutane 51 wadanda a da an yi garkuwa da su ne, ba a biya komai ba aka sako su.
Ya ce a yanzu haka 'yan sanda sun damka su gaba daya a hannun gwamnan jihar ta Zamfara, kuma nan ba da dadewa ba za a mika su ga 'yan uwansu.
A bayanan da ya yi ya kuma ya ce, nasarar ba ta tsaya a nan ba domin ana sa ran nan gaba ma za a sako wasu mutanen bisa wannan tattaunawa da hukumomin ke yi da 'yan bindigar.
Sannan ya ce a yanzu an samu raguwar hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a jihar ta Zamfara a dalilin tattaunawar da ake yi da su, wanda yana ganin idan tafiya ta kai tafiya matsalar tsaron da ke addabar jihar za ta zama sai tarihi.
Haka kuma wasu Fulani wadanda a da ba sa iya zuwa kasuwanni, a yanzu suna zuwa, domin ma yawanci kasuwanni a jihar sun bude, kamar yadda SP Shehun ya fada.
Jihar ta zamfara ta jima tana fama da matsalar tsaro lamarin da ya kai ga hallaka mutane da yawa da satar da dama domin karbar kudin fansa, lamarin da a baya-bayan nan ya fantsama wasu jihohin makwabtanta irin su Sokoto da Katsina.
Gwamnatin tarayyar Najeriyar ta sha bullo da matakan yaki da wannan matsala ta tsaro a jihar ta Zamfara, amma lamarin kusan ana ganin ya gagara duk da matakan tura sojoji da ake yi.