'Yan sanda sun tsare manyan mawakan Ghana biyu

'Yan sanda suna yi wa wasu mawaka biyu masu hamayya da juna tambayoyi, bayan da rikici ya barke a tsakaninsu a yayin wani bikin kide-kiden da aka yi a birnin Accra a kasar Ghana.
Jama'a da dama sun kalli bikin a talabijan wanda aka yi a daren ranar Asabar da ta gabata, inda aka bayyana mawaki Stonebwoy a matsayin wanda ya zama zakara a bana.
Jim kadan sai magoya bayan mawakan masu hamayya da juna Shatta Wale da kuma Stonebwoy suka fara hatsaniya.
Mutane sun yi mamaki sosai bayan da suka ga Stonebwoy ya fito da bindiga "domin kare kansa."
Wannan sabon abu ne a kasar Ghana.
Har ila yau 'yan sanda sun bayyana cewa sun kama mutum daya wanda ya yi amfani da hayaki mai barkono a lokacin rikicin.
A wata sanarwa, Stonebwoy ya ce: ''Ina son in ba da hakuri matuka, ina kuma yin da na sani da hannun da nake da shi a wannan rikicin, a wurin da ya kamata a ce an yi bikin wake-wake mafi girma a Ghana.''
Karanta wasu karin labarai











