Nigeria: 'Jakuna na fuskanatr barazanar karewa'

'Yan majalisar dokoki a Najeriya sun saurari ra'ayin jama'a kan yiwuwar yin kudurin doka da nufin bai wa Jakuna kariya daga safarar su da ake yi zuwa kasashen ketare.
A jiya majalisar wakilan kasar ta saurari ra'ayin jama'a karon na biyu inda kuma take shirin gabatar da shi dan zama kudurin doka, dan barazanar karewa da Jakunan ke fuskanta sakamakon safararsu ba bisa ka'ida ba.
Abdullahi Balarabe Salame, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwadabawa da Illela na jihar Sokoto, ya shaidawa BBC cewa daman wannan lamari daman ya dade ya na ciwa al'umar kasar tuwo a kwarya musamman a yankuna karkara da suka fi amfani da jakunan a matsayin abin sufuri.
Ana amfani da jakuna dan aikin gona, ko dora masa kaya zuwa kasuwa da debo ruwa a rafi, a wasu lokutan akan yi amfani da shi dan daukar marasa lafiya kamar mata masu juna biyu da kauyuka zuwa bakin hanya dan kai su asibiti.
Sai dai a yanzu jakunan na fuskantar barazanar safarar su zuwa kasashen waje, musamman kasar China da suke amfani da fatar sa dan yin wasu magungunan gargajiya.
Haka kuma ana amfani da kitsen sa wajen hada mayukan shafawa da mata ke amfani da su da akai amanna da cewa su na boye stufa wato maida tsohuwa yarinya.
'Yan majalisar na fatan da zarar an amince da dokar an kuma fara aiki da ita, za a fitar da jadawalin yadda za ta kasance da hukuncin da aka tanadar ga wanda duk ya take ta.






