'Teba na haddasawa matasa cutar Kansa'

Masu bincike a Amirka sun ce matasan wannan zamani na cikin hadarin kamuwa da cutar Cancer mai alaka da matsananciyar kiba, idan aka kwatanta da mutanen da aka haifesu a shekarun 1950.

Binciken da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, ta nuna yadda aka samu karuwar matasa da ake samunsu da nau'o'i 6 na cutar Cancer da kuma ake alakantawa da kiba.

Masu binciken sun karkare da cewa wannan bai rasa nasaba da nau'in abincin da ake ci, da ke haddasa teba idan akai la'akkari da irin wanda ake ci gwamman shekaru da suka gabata.

A karshe sun ce a halin da ake ciki matasa ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar, da kusan kashi 50 cikin 100 idan aka kwatanta da manyan da ke kokarin rage teba da wadanda ba su da tebar.