Jirgin sojin Najeriya ya yi hatsari a Damasak

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya rikito kasa yayin yaki da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun sojin kasar Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce daman jirgin mai saukar ungulu yana taimaka wa dakarun sojin kasa ne da ke yaki da 'yan Boko Haram lokacin da abin ya faru a garin Damasak da ke jihar Borno da maraicen jiya Laraba.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana musabbabin faduwar jirgin ba, da kuma mutanen da ke cikinsa lokacin da ya yi hatsarin, ko kuma an yi asarar rayuka, ko jikkata ba.

A baya-bayan nan sojojin Najeriya sun zafafa kai hare-hare maboyar 'yan Boko Haram, a yankin na arewa maso gabashin kasar.

Hakan na faruwa ne a didai lokacin da su ma 'yan Boko Haram, da mayakan da sukai mubaya'a ga myakan IS suke ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin.

Ana ci gaba da nuna fargaba kan yadda rashin tsaro ya sake kunno kai a jihar Borno da kewaye a daidai lokacin da Najeriya ke tunkarar babban zaben da ake sa ran za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.