Grace Mugabe: Afirka ta Kudu ta yi sammacin uwargidan Mugabe

Asalin hoton, Reuters
Hukumoni a Afirka ta Kudu na neman Grac Mugabe ta gurfana a gaban wata kotu domin amsa tuhumar da ake yi mata na cin zarafin wata matashiya mai tallata kayan kawa.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Afirka ta Kudu Vishnu Naidoo, ya tabbatar da bada takardar sammaci ga uwargidan tsohon shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe akan zargin cin zarafin wata matashiya.
Mr Naidoo ya bayyana cewa an bayar da takardar ne tun alhamis din da ta gabata.
Kafar dillancin labarai ta Reuters ta ruwaito cewa Mista Naidoo ya bayyana cewa 'yan sandan kasar na neman taimakon daga 'yan sandan kasa da kasa watau Interpol domin ganin cewa wannan takardar sammacin ta isa gareta.
Wannan yunkurin na bayar da takardar sammaci na zuwa ne bayan da a watan Yuli wata kotu a kasar ta soke kariyar diflomasiyya da Mrs Mugaben ke da ita.
Gwamnatin Afirika ta Kudu ta jawo cece-kuce bayan da ta kyale Misis Mugabe ta fita kasar bayan zargin ta da aka yi na cin zarafin wata matashiya a wani otel da ke Johannesburg.
Har yanzu, babu tabbacin ko Afirka ta Kudu za ta hukunta matar tsohon shugaba Mugaben.
Laifin dai da ake zarginta da shi ya auku ne wata uku kafin saukar Robert Mugabe daga kan mulkin Zimbabwe.










