An soke kwantiragin ginin filin jirgi a Saliyo

Gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da soke kwantiragin da ta bai wa kasar China na gina mata sabon filin jirgin sama da ya kai dala miliyan 400.
Ministan sufurin kasar Kabineh Kallon ya ce a yanzu ba sa bukatar sabon filin jirgi, don haka za a yi wa tsohon da ake amfani da shi kwaskwarima.
Ya ce tun da fari kowa ya san tsohuwar gwamnati ce ta bada kwantiragin gina filin jirgin saman na Mamamah, kuma Bankin duniya da asusun bada lamuni na duniya IMF sun soki matakin.
Sun nuna damuwa kan yadda ba shi ya yi wa Saliyo katutu, don haka babu amfanin gina filin jirgin.
A lokacin da sabuwar gwamnatin shugaba Julius Maada Bio ke yakin neman zabe ta yi alkawarin duba lamarin, don haka a yanzu an soke kwantiragin baki daya.
Tsohon shugaban Saliyo Earnest Bai Koroma ne dai ya bada aikin, wata guda gabannin zaben da bai yi nasara ba.







