Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutane 50 sun mutu a hadarin da tankar mai a Congo
Mutane 50 ne suka mutu a lokacin da wata tankar mai ta yi taho-mu-gama da wata mota a yammacin dimukradiyyar Congo.
Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Kinshasa kusa da gabar teku a Matadi, kuma nan take motar da ke cike da man fetur ta kama da wuta.
Gwamnan yankin tsakiyar Kpngo Atou Matabouna ya ce sama da mutane 100 ne suka kone, a lokacin da tankar ta fashe wuta kuma ta yi tartsatsi a wajen kuma gidajen da ke kusa su ma lamarin ya shafe su.
Jamhuriyar dimukradiyyar Congo ta sha fuskantar hadarin da manyan motocin dakon mai ke haddasawa.
Ko a shekarar 2010 mutane 220 ne suka mutu sakamakon mummunan hadarin da wata tankar mai ta yi a kusa da wani kauye da ke birnin Kisangani.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya kirga gawawwakin mutanen da suka kone sama da 50.
Shi ma wani likitan asibitin da ke kusa da wurin, da kuma aka kai maras lafiya asibitin ya ce an kawo wadanda suka kone don a ba su kulawar gaggawa kuma sun yi matukar konewa.
Sai dai wata kungiyar 'yan tawaye ta Lucha ta wallafa a shafinta na twitter, ta na sukar gwamnatin Congo, kan gaza kai daukin gaggawa a lokacin da lamarin ya faru.