Facebook na son inganta ayyukansa

Kamfanin Facebook na fuskantar suka bayan da wasu masu amfani da shafin na sada zumunta suka koka game da kin cire wasu bayanai masu nuna kiyayya da tayar da hankalin jama'a da ke kan shafin.

Mutanen sun ce sun bi dukkan ka'idojin da kamfanin ya tsara na shigar da koke, amma sun lura cewa kamfanin bai sauke bayanan ba, duk da alkawarin da yayi na magance matsalar take yanke.

A farkon makon nan ne wadanda suka samar da shafin Instagram suka sauka daga mukamansu saboda abin da suka kira rajin jituwa tsakaninsu da kamfanin Facebook.

A lokacin da suka kai kararsu - masu amfani da shafin na Facebook sun ce kamfanin yayi alkawarin daukar matakin sauke bayanan da ke na batanci ne, har ma ya gode masu domin bayyana matsalar da suka yi.

Amma kamfanin bai sauke su ba, kuma har yanzu suna nan, kuma kamfanin na Facebook ya kasa cewa uffan kan batun.

Wannan na cikin jerin matsalolin da shafin sada zumuntar mai farin jini ke fuskanta. Kevin Systrom da Mike Krieger su ne suka samar da shafin sada zumunta mai farin jini na Instagram, wanda kuma kamfanin Facebook ya saya a hannunsu a kan dala biliyan daya.

A farkon makon nan Kevin da Mike suka sanar da barin mukamansu a kamfanin saboda matsalolin da suka hada da rashin jituwa da kuma abin da suka kira dankarewar da kamfanin Facebook din yayi.

A nasa bangaren Facebook ya bayyana cewa yana masu fatan alheri, duk da cewa matakin na su ya zo wa kamfanin da bazata.