An samu sabani tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa

A jihar Zamfara da ke Najeriya rikici ne ya balle a jam'iyyar APC mai mulkin jihar, wanda ya kawo rabuwar kawuna tsakanin gwamnan jihar da mataimakinsa.

Hakan ya zo ne bayan da wasu daga cikin masu son jam'iyyar ta tsayar da su takara suka yi zargin cewa tuni gwamnan ya zabi wanda yake so ya gaje shi, kuma yake kokarin turasasa shi a kan al'umma, abinda ya sanya shi mataimakin gwamnan tare da wasu 'yan takarar guda bakwai suka ce hakan ba zai yiwu ba.

Mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakkala, ya shaida wa BBC cewa idan gwamna Abdul'aziz Yari ya zabi wanda zai gashe, ba zai hana wasu 'yan takara su tsaya ba.

Ya kuma yi zargin ba za a yi adalci kan salon zaben wakilai da ake son gudanarwa a zaben da ke tafe ba.

Hakzalika ya bukaci a gudanar da zabe na keke-da-keke, wato kato bayan kato idan har ana son yin adalci.

Kwamishinan yada labarai da walwalar al'umma na jihar Zamfara Sanda Muhammad Danjadi ya tabbatar wa BBC zargin da ake yi na cewa gwamnan yana da 'yan takara da yake goya wa baya.

Sai dai ya ce tun fil azal jihar tana amfani ne da tsari na fahimtar juna wurin fitar da yan takara.

Kuma sai da aka tattauna da shugabannin al'uma, da wakilai da masu ruwa da tsaki kafin gwamnan ya fitar da 'yan takarar da jama'a suka amince da su.

Ya musanta zargin da 'yan siyasa ke yi na cewa gwamnan Abdul'aziz Yari na yi wa siyasar hawan kawara da tilasta wa mutanen jihar yin abinda ba sa so ta bangaren fidda dan takarar da zai gaje shi.