Turkiyya: Erdogan na fuskantar babban kalubalen siyasa

An fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Turkiyya, kuma Shugaba Erdogan na fatan tsawaita wa'adin mulkinsa na wasu shekaru biyar wanda a lokacin ne zai karfafa ikonsa.

Amma yana fuskantar gagarumin kalubale a zaben shugaban kasa daga Muharrem Ince, wani dan siyasa mai sassaucin ra'ayi kuma mai matukar farin jini.

Turkiyya ba ta taba fuskantar irin wannan rabuwar kawuna ba a tarihinta. Haka kuma shi ma shugaba Recep Tayyib Erdowan bai taba fuskantar zabe mai wahalaswa kamar wannan ba.

A matsayinsa na shugaba mai cikakken iko, wanda ya zarce sauran shugabanni tun bayan mulkin uban kasar Kamal Ataturk.

Ana sa ran zai kara tara ma kansa karin karfin iko idan ya yi nasarar lashe wannan zaben - inda yayi alkawarin soke mukamin firai minista, da kuma rage ma majalisar kasar ikonta.

Amma idan ya kasa samun kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa, to dole ya fuskanci zage na biyu na zaben tare da Muharrem Ince, wani dan takara mai sassucin ra'ayi mai farin jini da ya sami karbuwa a wajen 'yan kasar.

A zaben 'yan majalisa kuwa, akwai wata gamayyar jam'iyyu da ke neman hana Mista Erdogan samun rinjaye a majalisa.

Magoya bayansa na matukar kaunarsa, amma abokan adawarsa suna nuna masa tsananin kiyayya.

Wannan ita ce ranar da Mista Erdowan ai fuskanci hukunci a wajen 'yan kasar ta Turkiyya, kuma babu wanda zai iya cewa ga yadda zaben zai kasance.