Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jirgin India ya wuce sararin Saudiyya zuwa Isra'ila
A wani mataki da ba safai ake gani ba, kuma mai cike da tarihi a karon farko jirgin sama mallakar India ya sauka a kasar Isra'ila da hanyar keta sararin samaniyar Saudiyya.
Ministan sufirin Isra'ila Yisrael Katz ya ce Air India ya taso ne daga birnin Delhi zuwa Tel Aviv, kuma shi ne na farko a hukumance ya fara sufuri daga kasarsa da Saudiyya wadda sam ba ta amince da Isra'ila ba.
Jirgin El Al dai ba ya sauka ko keta sararin Saudiyyar, dan haka ake ganin jirgin India zai bude sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Shi ma ministan yawon bude ido na kasar Yariv Levin ya ce amfani da sararin Saudiyya zai rage lokacin tafiya da sa'a biyu, da kuma rage kashe kudade.