Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kanawa ko Zazzagawa - Wa ya fi iya rubuta waka?
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ko wacce ranar 21 ga watan Maris don karfafa wa mutane gwaiwar ci gaba da rubutattun wakoki.
Manufar hakan dai ita ce, lalubo alfanun da tasirin da wakokin ke yi ga rayuwar al'umma ta fuskar zamantakewa da ilimantarwa da nishadi da sauransu.
An dade ana takaddama tsakanin Kanawa da Zazzagawa kan wadanda suka fi iya rubutattun wakokin Hausa.
A wannan makala, BBC ta ji ta bakin wasu mawaka biyu daga Kano da Zazzau.
Menene rubutattun wakoki?
Wake, ko rubutattun wakoki, wasu hanyoyi ne na fito da abin da ke kunshe a cikin zuciyar dan adam ya bayyana a fili.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, tun tale-tale, rubutattun wakoki kan nuna yadda bil-Adama suka yi tarayya da juna.
A kasar Hausa ma rubutatun wakoki kan taka muhimmiyar rawa wajen ilmantarwa ko fadakarwa ko zaburar da al'umma.
Wasu 'yan Najeriya da BBC ta zanta da su, sun shaida mata su na daukar darussan rayuwa daga cikin rubutattun wakokin fitattun mutane kamar Marigayi Sa'ad Zungur da sauransu, wadanda yawancin wakokinsu kamar fadakarwa ne, da nuni ga aikata halin kwarai da gujewa munanan dabi'u.
Masana sun bayyana cewa wata matsala da ake fuskanta a zamani ita ce, matasa ba su san muhimmancin rubutattun wakokin mashahuran mutanen da suka ci gajiyar halayyar kwarai da zamantakewa tsakaninsu da makofta da al'umma ba.
Hasali ma yawanci, ba su cika damuwa da saurare ko karanta wakokin da aka gada tun iyaye da kakanni ba.
Albarkacin wannan rana ce BBC Hausa ta ji ta bakin wasu da ke rubutattun wakoki a zamanin don jin abun da ya sa suke sha'awar wannan fanni:
Bashir Yahuza Malumfashi
Sunana Bashir Yahuza Malumfashi. An haife ni a garin Malumfashi, Karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, Najeriya shekara 51 da ta gabata.
Ni dan jarida ne, a yanzu haka ni ne Editan Labarai na jaridar Aminiya.
Baya ga kasancewata dan jarida, ni marubuci ne kuma sha'iri. Ina rubuta kirkirarrun labarai da kuma wakoki a cikin harsunan Ingilishi da kuma Hausa.
Tun ina aji uku a sakandare, wato a 1983, na fara rubutu. A fannin rubutun waka kuwa, na fara rubuta ta Hausa a shekarar 1987, ta Ingilishi kuma a 1994 na fara.
Ya zuwa yanzu na rubuta wakoki fiye da guda 200, kuma ina sa ran ya zuwa karshen shekarar nan zan wallafa su, in samar da littattafai biyu, daya na Hausa, daya kuma na Ingilishi.
A cikin wakokin da na rubuta, Bakandamiyata ita ce wacce na yi wa Manzon Allah, Muhammadu (saw), wacce na sanya wa suna "Sha Yabo: Muhammadu (saw)."
Muhimmancin rubutattun wakoki
Dalilin da ya sanya nake rubuta waka shi ne, saboda fadakarwa, ilimantarwa da kuma nishadantarwa.
Ta hanyar waka ina samun nishadi da gamsuwa, kuma ta hanyar waka ina samun kaifafa tunanina da kara wa kaina azamar neman ilimi. Ta hanyar waka, ina ba ruhina abinci. Ko da ina cikin bacin rai, idan na dauki biro da takarda, na fara rubuta waka sai in ji bakin cikina ya gushe.
Tasirin rubutattun wakoki
Babu shakka tasirin waka yana da yawa, domin kuwa al'amari ne da ya samu fandeshi tun shekaru aru-aru masu yawa. Ko a tarihi, kafin zuwan Manzon Allah (saw), Larabawa sun shahara wajen rubuta wak'a. Har gasa suke yi a zamaninsu.
A lokacin nan, jarumtaka na ga gida ko zuri'ar da suka shahara a wak'a. Ta hanyar wak'a, ana adana harshe, ana bunk'asa shi kuma ana ilimantarwa da fad'akarwa da nishad'antarwa.
Misali, shahararrun mawak'a da suka bayar da gudunmowa ga al'umma da har yau ake cin gajiyarsu, sun had'a da Mujaddadi Shehu Usman 'Danfodiyo da d'iyarsa Nana Asma'u da Sarkin Zazzau, Aliyu 'Dansidi.
Na bayansu kuma, akwai su marigaya Malam Sa'adu Zungur, Malam Mudi Spikin, Malam Sani Dangani, Abubakar Ladan, kai har ma da tsohon Shugaban K'asa, Alhaji Shehu Aliyu Usman Shagari.
Wak'a za ta ci gaba da yin tasiri a cikin al'umma har zuwa k'arshen duniya.
Bakandamiyar Bashir Yahuza Malumfashi
- Sha Yabo: Muhammadu (SAW)
- Ya Allah Ka ba ni basira
- Rarraba mu da dukka asara
- Zan yabon mai hana tijara
- Sha yabo tuli ya sahara
- Almustapha 'Daha Muhammad
- Assalamu alaika Nabiyyu
- Shugaban dukkan anbiya'u
- Hashimiyyu K'uraishiyyu
- Kai ne badadin Ya Alhayyu
- Jinjina gare ka Muhammad
- A halittu ba ka da tamka
- Kyakkyawa ko ba wanka
- Babban danni mai tanka
- Girmanka ya wuce jinka
- Sayyadi Rasulu Muhammad
- Kai maliya ka wuce gulbi
- Tsarki gare ka a k'albi
- Aikinka gyaran k'albi
- Tauraro ka wuce halbi
- Baban Ruk'ayya Muhammad
- 'Dan Amina ka wuce daro
- Ran Litinin kag gangaro
- Ba kuka ba wani b'aro
- Sai murmushi ka k'aro
- Ya Aminu namu Muhammad
- Na Khadijah babban gwarzo
- Ga baituka naka murzo
- Bisa izza duk na furzo
- Maki'yanka ni zan gurzo
- Ya Habibu namu Muhammad
- Ka fi ruwan sanyi a bazara
- Kyauta wurinka ba tazara
- Kyan d'aki sai da azara
- Murmushi kullum ka zizara
- Na A'isha jigo Muhammad
- Ka fi zuma zak'i ko madara
- Kai kake izza ga mahara
- Ja'irai sun zam a makara
- Ba su da riba sai dai takura
- Na Maimuna Maula Muhammad
- A hak'uri ka zarce d'an damo
- Ba ka murna da k'ank'amo
- Mai k'aunarka ya kandamo
- Alheri za ya fantamo
- Maigidan Hafsat Muhammad
- Ya Allah Ka k'ara baiwa
- Da ni'ima wadda Kai wa
- Ibrahim mai adawa
- Da shirka ba ya halwa
- Ga abban Zi Muhammad
- Ya Allah Ka k'ara salati
- Ga abban Nana Fati
- Muna murna da party
- Har ma mun rera baiti
- Ga 'Daha guda Muhammad
Sulaiman Salisu Muhammad
Sunana Sulaiman Salisu Muhammad Mai Bazazzagiya. Ni mazaunin Unguwar Maigwado Sabon Garin Zariya ne. Bayan na gama karatun Firamare da Sakandare na shiga Kwalejin Zurfafa Ilmi da ke Zariya.
Bayan na kammala na samu damar wucewa zuwa Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, inda na karanci harshen Hausa; na kammala a 1995.
A shekarar 2000 na samu shiga Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya domin yin digirina na biyu a harshen Hausa, fannin rubutacciyar waka.
Na karantar a wata makarantar sakandare a Abuja da kuma Kwalejin Ilimi ta Gamnatin Tarayya (FCE) da ke Zuba kusa da Abuja. Na kuma karantar a Kwalejin Ilimi ta Gamnatin Tarayya da ke Zariya.
Yanzu ina koyarwa a Sashen Harsunan Najeriya da Kimiyyar Harshe a Jami'ar Jihar Kaduna.
Dalilan rubuta waka
Ina rubuta waka saboda dalilai da dama, manya daga ciki su ne:
1. Sha'awa—Kila ko na yi ta'aziyya ko na ga wani abu ya burge ni, sai na yi waka don yabo ko wani abu makamancin wannan;
2. Domin biyan bukatar zuciya — idan na shiga damuwa, wani abu ya damlamle min, nakan samu sauki idan na rubuta a kan abin, kamar lokacin da gama makaranta ban samu aiki ba, sai na rubuta wata waka da na sanya mata suna "Tsurkun Boko", wato kamar na gama boko amma ga shi ba ni da aiki.
Sannan akwai wadda na sanya mata suna "Kishi Kumallon Mata", ita kuma saboda na nemi aure ne aka kasa ni; sannan kuma kamar mako uku da suka wuce na je Kano sun gayyace ni na gabatar da wata Makala, ina gama gabatar da makalar aka sace min waya.
To na ji haushin abin, saboda haka na rubuta "Ta'aziyyar Wayata". Karanta wakar da na yi ya sa na samu sa'ida a zuciyata;
3. Domin fadakarwa ko gargadi ko koyarwa ga al'umma — akwai abubuwa da ke faruwa a tsakanin al'umma idan na dube su sai na yi rubutu don fadakarwa game da illolinsu ko alfanunsu, misali shaye-shaye, ko muhimmanicn ilimi ko satar jarabawa da dalibai ke yi, da sauranu
4. Sannan nakan yi na addini.
Bakandamiya
Bakandamiyar wakokina ita ce Bazazzagiya.
A shekarar 2009 mun je taron wata kungiyarmu ta Gizago a Kano. To akwai wasa tsakanin Zagezagi da Kanawa. Kanawa suna cewa: "Ko da me ka zo an fi ka."
To sai na mike na ce na zo da wakata mai suna Bakuraishiya a lokacin (a jaridar Aminiya aka mayar da ita Bazazzagiya saboda ta kare da "ya"), idan akwai Bakanon da ya taba rubuta irinta ina bukata.
Sai aka rasa; sai suka ce a ba su lokaci za su rubuta. Sai jaridar Aminiya ta buga wannan kalubalen.
A takaice ba su iya ba sai bayan wajen shekara uku 2011. A lokacin baiti 300 ne. A yanzu wakar ta kai baiti 700.
Akwai wani Bilyaminu Zakariya Ayagi ya yi baiti 500. Aminu Ala ya yi baiti 300. Duk da yake Ado Gidan dabino yana cewa Aminu ALA ya yi baiti 1000 ne, amma idan na ce a kawo ta, har yanzu babu.
Wakar tana tafiya ne da dango dai-dai dukkanta. Sannan babu maimaicin kalma a karshen dango.
Bilyaminu Zakariyya Ayagi
Sunana Bilyaminu Zakariyya (Abul-warakat Ayagi). An haife ni a unguwar Ayagi cikin karamar hukumar Dala, a birnin Kano.
Na yi karatuttuka na addini da na zamani daidai gwargwado, ina ma kan yi. A yanzu haka ina aikin koyarwa da rubuce-rubuce.
Dalilin rubuta waka
An ce wanda ya fi amfani a cikin al'umma shi ne wanda yake amfanar da al'umma.
Saboda haka ina yin waka ne don na duba na ga ba abin da zan iya amfani da shi wajen bai wa al'ummata gudunmawa a fagen ilmantarwa, nishadantarwa da fadakarwa kamar rubuta.
Bakandamiyata ita ce "Alu-Ja", wadda take cikin kundina na "Taba Ka Lashe".
Dalilin rubuta ta kuwa tsananin kaunar masoyina Annabi Muhammadu ne da ta motsa min.
Tasirin rubutattun wakoki
Waka na tasiri wajen canja alkiblar jama'a, a isar musu da ilimi a wake, su kuma hau gwadaben da ake bukata.
Mai bukatar nishadi ma a wake zai sami biyan bukata. Shi ya sa a tarihin kowace al'umma waka na sahun gaba.
Bakandamiya
Bakandamiyata ita ce wakar "Alu-Ja", wadda ke cikin kundina na "Taba Ka Lashe":
Waye isasshe mai isar da dukan isa * Wannan da Rabbi a donsa yai kai har da ni?
Waye karaf da sani abin so? Tambaya: * Dan lele gun Allah da bai wa ko kani?
Waye magaga saman sama'u na Bubakar? * Shi ne ga duk cuta ya zamto magani
Waye Alu-ja kokuwar duk daukaka? * Wannan da sonsa ya tsaga hantata, jini
Shi ne MUHAMMADU dan AMINATU da wurin * ABDALLA hasken duniya har zamani
Kyawunsa fes, bakinsa tas da idonsa fes * Manzonmu fes, matsayinsa cif, mai kyan gani
*** *** ***
Ba don ba kogi kan kafe wataran kuwa * Ambaliyar barna yakan yi a zamani
Da sai na ce kyautarsa tamkar SHUGABA * Amma ina, gurgu da tsere a sansani
Kin makkaro rana, kusufi ga yawan * zafinki mai radadi da tarin razani
Da sai na ce haskenki ya kusa yai kama * Da na Al'aminu, matsa ki yo nisa ga ni
Ita ma saman ba don akwai wata daukaka * A gabanta wadda ta sa nake ta tunatuni
Da sai na ce ta dan kama da isarsa ai * Amma ina ko tai dage matsawar yini
Sarkin tawali'u. Ke kasa ba don akwai* Nau'i na kaskanci gareki ba tun tuni
Da sai na ce saura kiris kiy yo kama * Da tawali'un Manzonmu Abdulmumini
Na waiga dukkan daukaka, in zan hada * Da ta Mustafa sai in ji kunyar yin kini
Don sai na ganta kamar digo bisa maliya * Tamkar akwai a hada da babu a yo sani