Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ta shiga na'urar tantance kaya don kada a yi ma ta sata
Wata 'yar China ta bi sawun kayanta a na'urar tantance kaya a tashar jirgin kasa, domin gudun kada a sace mata kaya a wajen bincike.
Lamarin ya ba ma'aikatan tashar jirgin sama a kudancin China mamaki bayan da na'urar bincike ta nuna hoton matar.
An nuna yadda al'amarin ya faru a ranar Lahadi a wani bidiyo a intanet, a daidai lokacin da mutanen China ke gaggawar zuwa bikin sabuwar shekararsu.
Matar ta duba kayanta ne sannan ta fice.
Hotonan na X-ray sun nuna matar ta duka da hannayenta da kafafu kusa da kayanta, sanye da takalmi mai tsini.
Babu dai tabbas ko matar ta damu da kayanta ne, amma yawancin mutane a China na daukar kaya da yawa a lokacin da suke tafiye-tafiye domin bikin sabuwar shekara a kasar.
An shaida mata cewa dole sai jikar kayayyakinta sun bi ta hanyar na'urar da ke tantance kaya, amma ta ki yarda.
Nan take ta yanke shawarar ta bi kayanta a na'urar, al'amarin da har ya ba wasu jami'an da ke aikin tsaro a tashar dariya.
Hukumomin tashar jirgin kasa a Dongguan sun sha bai wa fasinjoji shawara kan su kauracewa hawa na'urar tantance kayan, saboda tururin da ke fita na iya haifar da illa.
Matar na cikin mutane miliyan 390 da aka kiyasta za su tafi hutun sabuwar shekara a China ta hanyar jirgin kasa, wacce ta fado a ranar 16 ga Fabrairu.