Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
"An yi wa masu jego fyade"
Ministan lafiya na Kenya, Cleopa Mailu, ya bayar da izinin a gudanar da bincike akan wasu mata da suka yi ikirarin anyi musu fyade a babban asibitin da ke babban birnin kasar Nairobi.
Mr Mailu ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa,"Yana sane da zargin da ake na yi wa wasu mata da suka yi sabuwar haihuwa fyade a hanyarsu ta fitowa daga dakin haihuwa". Kamar yadda batun yake ta yawo a shafukan sa da zumunta da muhawara.
Wani mai amfani da shafin Facebook ya bayyana cewa "an far wa masu jegon ne a hanyarsu ta zuwa wurin jariran nasu don su ba su nono, inda aka ajiye jaririn a wani gini na dabam.
"Samun tsaro muhimmin al'amari ne musamman ga matan da jariransu suke dakin rainon yara. Dakin rainon jariran na kasa ya yin da dakin masu haihuwar yake hawa na uku.
"Matar ta tafi ne zata ba wa jaririnta nono misalin uku na dare. Ihun da matar tayi ne kawai ya ceceta.
"Anyi wa matar tiyata ne aka cire mata 'yan biyu, amma ba ta gama warkewa ba. Kuma irin wannan matan na bukatar kariya," in ji sakon na Facebook.
Batun ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta daga wurin mutanen da abun ya shafa ko suka san wadanda abun ya faru da su.
Minstan lafiyar ya ba wa hukumar asibitin umarnin tsaurara tsaro a asibitin kuma su gabatar mishi da rahoto kan batun ranar Litinin.