Shin Facebook na da illa ga lafiyar kwakwalwa?

Mark Zuckerberg, shugaban Facebook

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg

Kamfanin Facebook ya bayar da sanarwar cewa zai yi wani babban sauyi a shafin domin cimma cikakkiyar hulda mai ma'ana a tsakanin masu amfani da shafin.

Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg ya ce bayanai daga shafukan kasuwanci da kafofin sada zumunta na dakushe damar hulda tsakanin mutane wanda kuma a cewarsa dama ce da ke da matukar muhimmanci.

Don haka ne ya ce sauye-sauyen da za a yi za su sa mutane su rage yawan lokacin da su ke batarwa a kan shafin kuma lokacin zai zama mai daraja.

Facebook ya fuskanci matsin lamba a kan yadda shafin ya ke iya zama jaraba ga wasu da kuma yiwuwar illarsa ga lafiyar kwakwalwa.

Kamfanin ya ce a sanadiyar wanna sauyin, mutane zasu rage ganin tallace tallace da sakonni daga kamfanoni.