Zaben 2019: 'Atiku da El-Rufai na sha'awar takara'

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun ce rikicin da ya barke tsakanin tsohon mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna wata alama ce da ke nuna cewa an soma buga gangar siyasar shekarar 2019.

Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin jiga-jigan jam'iyyar ta APC mai mulkin ne sakamakon zargin da suke yi wa juna da aikata laifuka daban-daban.

Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar yana yin zagon-kasa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

El-Rufai na yin raddi ne ga zargin da Atiku ya yi cewa shi butulu ne, kuma ya saba wa ka'idojin aikin gwamnati a lokacin da yake rike da mukamai a gwamnatin Olusegun Obasanjo.

A wata hira da Premium Times ta wallafa, Atiku ya ce shi ya shigar da El-Rufai gwamnati har ya zama minista, amma da shi "aka yi amfani wurin zargina da cin hanci", abin da kotu ta wanke ni daga baya.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, gwamnan El-Rufai ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa sun dabaibaye Atiku, abin da ya sa yake tsoron zuwa Amurka.

'An ja zare'

Amma a wata hira da ya yi da BBC, Dr Abubakar Kari na Jami'ar Abuja, ya ce rikicin da ke tsakanin mutanen biyu tamkar share fage ne ga harkokin siyasar shekarar 2019.

A cewarsa, "An fara gwagwarmaya ce ta takarar shugabanci a zaben shekarar 2019. Ana rade-radin cewa El-Rufai da Atiku dukkan su suna sha'awar yin takara.

Abin da wannan hayaniya tasu ta nuna shi ne kowannen su yana neman gindin-zama ne."

Ya kara da cewa duk da yake Shugaba Muhammadu Buhari bai taba cewa ba zai tsaya takara a 2019 ba, wasu na ganin ya tsufa don haka zai iya ja da baya domin wasu su karba.

Kuma aganinsa hakan ne ya sa El-Rufai da Atiku ke son nuna wa duniya cewa a shirye suke su maye gurbin Shugaba Buhari.