Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Raheem Sterling, Gabriel Jesus, Cristiano Ronaldo, Conor Gallagher
Real Madrid na son saye ɗan wasan Manchester City da Ingila mai buga gaba Raheem Sterling, mai shekara 27, bayan watsa mata kasa a ido da ɗan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekaru 23 ya yi. (Star)
Tottenham za ta kalubalanci abokiyar hamayarta Arsenal wajen cinikin ɗan wasan Brazil Gabriel Jesus daga Manchester City. (Telegraph)
Spurs na dab da daidaitawa da ɗan wasan Southampton da Ingila, mai tsaron raga Fraser Forster da ke da shekara 34. (Mail)
Erik ten Hag ya bayyana karara cewa yana son ɗan wasanPortugal mai buga gaba Cristiano Ronaldo, ɗan shekara 37, ya cigaba da zama a Manchester United a kaka mai zuwa. (Metro)
Ɗan wasanLeicesterYouri Tielemans, mai shekara 25, na daya daga cikin mutanen da kocin Arsenal Mikel Arteta ke farauta a sahun gaba. (Telegraph)
Gunners za ta yi kokarin sayar da 'yan wasanta bakwai a wannan kaka, ciki harda ɗan wasan Sifaniya da ke buga baya Hector Bellerin da mai tsaron raga Bernd Leno. (Sun)
Juventus ta matsa kaimi kan ɗan wasan Arsenal Brazil Gabriel, mai shekara 24. (Mirror)
Kocin Napoli Luciano Spalletti ya jadada cewa kungiyar ba za ta iya sayar da ɗan wasansu mai shekara 30 da Chelsea ke hari dan asalin Senegal ba, Kalidou Koulibaly. (Star)
Leeds ta shirya daidaitawa da ɗan wasan Amurka da ke taka keda a Red Bull Salzburg, Brenden Aaronson, mai shekara 21, kan yarjejeniyar fam miliyan 23. (Times)
Patrick Vieira ya ce Crystal Palace za ta so ta dauko matashin ɗan wasa mai shekara 22 da ke buga wa Ingila tsakiya Conor Gallagher daga Chelsea a sabuwar kaka. (Star)
Marcos Alonso, ɗan shekara 31, ya bukaci ya bayar Chelsea karkashin yarjeniyar da aka cimma da shi kafin ya je Barcelona. (Sport - in Spanish)
Everton da Leicester sun shiga sahun masu farautar ɗan wasan Burnley da Ingila James Tarkowski, mai shekara 29. (90 min)
Newcastle na sanya ido kan ɗan wasanAtletico Madrid Renan Lodi, da ke taka leda a Brazil. (Chronicle)
Dan wasan Chelsea Andreas Christensen, mai shekara 26, na gab da koma wa Barcelona nan da 'yan kwanaki. A watan Yuni kwantiraginsa ke karewa a Stamford Bridge. (AS - in Spanish)
Mai bugawa Denmark tsakiya Christian Eriksen, ɗan shekara 30, ya samu tayi daga ƙungiyoyin Firimiya uku yayin da zamansa na gajeren lokaci a Brentford ke kawo karshe. (Fabrizio Romano)
David Moyes cikin yanayi na fusata ya sake suka duk da kokarin da West Ham da suka yi.(Standard)