Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AC Milan ta lashe kofin Serie A karon farko bayan kaka 11
AC Milan ta yi nasarar daukar Serie A na bana kuma na 19 jumulla, wanda rabon da ta lashe kofin tun bayan kaka tamauala 11.
Milan din ta yi nasarar doke Sassuolo 3-0 a wasan mako na 38 a babbar gasar tamaula ta Italiya.
A minti na 17 da fara tamaula Olivier Giroud ya ci kwallo, sannan ya kara na biyu a minti na 32, minti hudu tsakani Franck Kessie ya kara na uku a raga.
Tun farko magoya bayan Milan ba su yi murnar daukar koci, Stefano Pioli ba a 2019, kawai don ya taba horar da Inter Milan abokiyar hamayya.
Sai dai hakan bai hana shi gudanar da aiki ba, har ta kai ga ya lashe kofin bana da tazarar maki biyu tsakani da Inter Milan.
A ranar ta Lahadi Inter ta casa Sampdoria 3-0 karkashin jagorancin Simone Inzaghi, wadanda suka yi fatan ko AC Milan za ta barar da dama, hakan bai samu ba.
Kungiyar Napoli ce ta uku, bayan da ta doke Spezia 3-0, Juventus ce ta karkare a mataki na hudu a gasar bana.
Massimiliano Allegri - wanda ya ja ragamar Milan ta dauki Serie A a 2010/11, shi ne kocin Juventus a yanzu da za su buga Champions League a badi.
Milan ta dade tana jiran wannan ranar da za ta lashe Serie A tun bayan 2011 da Allegri ya ci mata kofin.