Chelsea ta kasa doke manyan kungiyoyin Premier biyar duk da cefane mai tsada a bana

Ranar Lahadi Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 3-1 a Stamford Bridge a wasan mako na 17 a gasar Premier League.

Rashin nasarar da kungiyar ta yi ya sa ta koma ta takwas a teburi da maki 26, bayan buga wasa 17 a kakar bana.

Kuma karawa ta biyar kenan da aka doke Chelsea a Premier, bayan cin wasa bakwai da canjaras biyar da cin kwallo 32 aka zura mata 21 a ragarta a gasar ta bana.

Tun da aka fara kakar bana masu sharhin wasanni suka sa Chelsea tana daga cikin kungiyar da za ta kalubalancin Liverpool da Tottenham wajen lashe kofin Premier League na kakar 2020/21.

Sai dai kuma alkalumma sun sauya tun bayan da Everton ta yi nasara a kan Chelsea ranar 12 ga watan Disamba, wadda ta kawo karshen wasa 17 da kungiyar ta Stamford Bridge ta yi a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba.

Tun kashin da Chelsea ta sha a Goodison Park, kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Wolvrhampton da Arsenal da kuma Manchester City da yin canjaras da Aston Villa da doke West Ham United.

Cikin maki 18 da ya kamata Chelsea ta hada da ƙyar da gumin goshi ta samu hudu, kuma a lokacin Sheffield United ta yi rashin nasara wasa shida sai West Brom da biyar sai Chelsea da ta sha kashi a wasa hudu.

Chelsea ta fada wannan halin bayan da a farkon kakar bana masu tsaron bayanta sun sa makulli sun rufe ko ina, amma yanzu sun zama rariya, kuma wadanda suke ci wa kungiyar kwallo kawo yanzu sun kasa tabuka abin azo a gani.

Chelsea ta yi cefanen da ya kai Yuro miliyan 247 fiye da kowacce kungiya a Turai a bana, kuma a lokacin da cutar korona ta nakasa tattalin arzikin kwallon kafa a fadin duniya.

Fitattun ƴan wasan da Chelsea ta ɗauko

Cikin fitattun 'yan kwallon da Chelsea ta dauka a sun hada da Kai Havertz kan Yuro miliyan 80 da Timo Werner kan Yuro miliyan 53 da Ben Chilwell kan Yuro miliyan 50 da Hakim Ziyech kan Yuro miliyan 40 da Edouard Mendy kan Yuro miliyan 24 da fitatcen mai tsaron baya, Thiago Silva.

Shi dai Havertz ya kasa komawa kan ganiya tun bayan da cutar korana ta damke shi, shi kuwa Werner ya yi wasa 12 ba tare da ya ci wa Chelsea kwallo ba, karon farko da ya dauki lokaci bai zura kwallo a raga ba tun da ya fara tamaula a Stuttgart a 2014/15

Tun da aka fara wasannin Premier League na bana, Chelsea ba ta yi nasara a kan manyan kungiyoyin Premier biyar ba da suka hada da yin duro da Manchester United da kuma Tottenham, yayin da Liverpool da Arsenal da kuma Manchester City suka doke ta.

Chelsea za ta fuskanci kalubale nan gaba idan ba ta koma kan ganiya ba, ganin za ta fafata da Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu a Champions League.

Ita dai Atletico tana jan ragamar teburin La Liga, bayan da ta doke Deportivo Alaves ranar Lahadi, tana kuma da kwantan wasa biyu a La Liga.