Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Henderson, Giroud, Eriksen, Wilder

Golan Manchester United Dean Henderson, mai shekara 23, zai nemi tafiya zaman aro domin a shekara mai zuwa ya samu damar buga wa Ingila gasar European Championships, a yayin da ake cewa Leeds da Brighton na son sa a watan Janairu. (Sun)

Manchester City ta daina zawarcin dan wasan Barcelona da Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, a cewar kwararriyar mai sharhi kan wasanni a Sifaniya Semra Hunter. (Sky Sports)

Dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 34, ya amince cewa rashin buga wasa a Chelsea "abin damuwa ne" kuma zai yanke hukunci kan makomarsa a watan Janairu. (Mirror)

Tsohon dan wasan Tottenham Christian Eriksen, mai shekara 28, yana da damar barin Inter Milan a watan Janairu, a cewar babban jami'in kungiyar kwallon kafar ta Italiya Beppe Marotta. (Goal)

Manchester United za ta iya soma zawarcin Eriksen. (Corriere dello Sport, via Star)

Arsenal ta samu tagomashi a fafutukarta ta neman daukar dan wasan tsakiyar Turkiyya Yusuf Yazici bayan wakilinsa ya amince cewa dan wasan na Lille na son manyan kudade. An kwatanta dan wasan mai shekara 23 da Mesut Ozil, mai shekara 32, wanda Gunners ta daina ɗasawa da shi. (Mirror)

Raunin da dan wasan Barcelona dan kasar Sifaniya Gerard Pique, mai shekara 33, ya ji zai iya sauya yadda kungiyar za ta shiga kasuwar cinikayyar 'yan kwallon kafa a watan Janairu domin neman sabon dan wasan tsakiya. Kungiyar ta jima tana son daukar dan wasan Manchester City Eric Garcia, mai shekara 19. (Manchester Evening News)

Pique zai nemi shawara karo na biyu kan raunin da ya ji daga wurin Dr Ramon Cugat, kwararren kan ciwon gwiwa a Barcelona. (Sport)

Babban jami'in wasa naBarcelona Ramon Planes zai gana da kocin kungiyar Ronald Koeman domin tattaunawa kan zabin da suke da shi game da musayar 'yan wasan da ke tsaron baya. (Marca)

Ana rade radin cewa dan wasan Rennes da Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 21, zai tafi Tottenham kuma ya ce yana son tafiya babar kungiya, ko da yake ya kara da cewa ba matsala idan ya ci gaba da zama a inda yake. (Football London)