Kasuwar Cinikin 'yan wasa: Makomar Upamecano, Varane, Wijnaldum, Man City, Alaba, Anderson

Liverpool da Manchester United sun sami damar sayo dan wasan RB Leipzig Dayot Upamecano wanda dan kasar Faransa ne, kuma a watan Janairu za a yanke hukunci kan inda zai nufa tun da Bayern Munich ba za ta iya sayen dan wasan mai shekara 22 da haihuwa ba. (Bild, via Mirror)

Manchester Unitedna da damar sayen Raphael Varane, dan wasan baya na kasar Faransa mai shekara 27 daga Real Madrid. (Manchester Evening News)

Real Madridza ta yi takara da Barcelona domin dauko Georginio Wijnaldum, dan kasar Netherlands, kuma mai shekara 31 daga Liverpool. (Corriere Dello Sport via Sport)

Lionel Messi ya sanar da Manchester City aniyarsa ta komawa can bayan da dan kasar Ajentinan mai shekara 33 ya yi korafin "gajiya da zama mai janyo matsala a kungiyar Barcelona". (Express)

Dan wasan Bayern Munichda Austria, David Alaba mai shekara 28 shi ne dan wasan da Real Madrid ta fi son sayowa idan Sergio Ramos ya bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana. (AS)

Dan wasan West Ham da Brazil Felipe Anderson mai shekara 27 na iya komawa kungiyar daga Porto inda aka bayar da shi aro idan kungiyar kasar Portugal din ta sake sayo dan wasanta na da wato Hulk daga Shanghai SIPGa watan Janairu. (Record - in Portuguese)

Da alama Barcelona na daf da sayo Eric Garcia, dan wasan baya na kasar Sfaniya mai shekara 19 saboda Manchester City ba za su kara ko kwabo ba kan tayin fam miliyan 17.8 da su ka yi domin sayen dan wasan. (Marca)

Arsenal ta amince ta sayo dan wasan kasar Tunisiya da kuma Hertha Berlin wato Omar Rekik mai shekara 18 a watan Janairu. (Football London)

Sevilla da Hertha Berlin na sha'awar dauko Julian Draxler mai shekara 27, wanda dan wasan Paris St-Germain ne, kuma dan kasar Jamus. (Calciomercato - in Italian)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ba 'yan makarantar koyon kwallon kafa na kungiyar su takwas damar burge shi yayin mako guda da kungiyar ta ware domin tace 'yan wasan a wannan lokaci da ta ke fuskantar kalubale saboda 'yan wasanta da dama sun sami raunuka. (Mirror)